Tsohon Gwamnan Jihar Kano, Malam Ibrahim Shekarau, ya bayyana cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf na da cikakken ‘yancin sauya sheƙa daga Jam’iyyar NNPP zuwa APC, idan ya ga hakan ya dace da muradunsa na siyasa da kuma bukatun al’ummar da ya ke jagoranta.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ina-tuna-doguwar-tafiyar-siyasa-da-rikon-amana-tsakaninmu-kwankwaso-ya-taya-gwamna-yusuf-murnar-zagayowar-ranar-haihuwarsa/
Shekarau ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai inda ya jaddada cewa sauya jam’iyya a tsarin dimokuradiyya abu ne da kundin tsarin mulki bai haramta ba, kuma ba a daukarsa kai tsaye a matsayin cin amanar jama’a.
Ya ce misali Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, wanda ya taba barin PDP zuwa APC a lokacin da yake gwamnan Kano ba tare da ajiye mukaminsa ba, ya kafa hujjar da ke nuna cewa gwamna na iya sauya jam’iyya tare da ci gaba da rike kujerarsa.
A cewarsa, sukar da ake yi wa Gwamna Abba Kabir Yusuf kan yiwuwar sauya sheƙa ba ta da tushe mai karfi, kasancewar irin wannan lamari ya taba faruwa a siyasar Kano da Najeriya baki daya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/fubara-ne-jagoran-apc-a-jihar-rivers-in-ji-apc-a-matakin-kasa/
Shekarau ya kara da cewa shawara ta karshe ta rataya ne a wuyan Gwamna Abba Kabir Yusuf, wanda ya kamata ya yi la’akari da ra’ayin jama’a da kuma tasirin matakin ga zaman lafiya da ci gaban jihar Kano, yana mai cewa sauya jam’iyya lamari ne na siyasa, ba na shari’a kai tsaye ba.
Yace kafin zaben 2023 Kwankwaso bayan ya bar PDP ya koma APC ya sake barin APC ya koma PDP daga baya kuma ya koma NNPP duk a dan lokaci kadan a dan haka babu dalili na Kalubalantar Gwmana Abba

