Daya daga cikin jajirtattu kuma mai fada aji a cikin jam’iyyar (APC) Muhammad Kabir Sani Hotoro ya gargadi Ministan Abuja Nyesom Wike da ya daina tsoma baki a cikin harkokin APC tunda shi ba dan jam’iyyar ba ne.
Hotoro yace ba zaiyi shuru ba a yayinda Wike ke ƙoƙarin lalata ginshiƙan da jam’iyyar ta dogara a kansu.
TST Hausa ta rawaito cewa Kalaman batanci da Ministan Babban Birnin Tarayya Nyesom Wike, ya yi wa Sakataren Jam’iyyarAPC na Ƙasa, Sanata Ajibola Basiru, ba sabani na siyasa kawai ba ne,barazana ce kai tsaye ga ikon jam’iyya da mutuncin tsarin APC.
Yace Wannan lamari ba rikicin mutum ɗaya ko na yankin Rivers ba ne.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ka-ajiye-mana-kujerar-mu-ta-minista-ka-mayar-da-hankali-kan-siyasar-rivers-tunda-ita-kafi-so-apc-ta-garga%c9%97i-wike/
Hotoro yace al’amari ne da ya shafi APC gaba ɗaya.
Sannan yace hakan Ƙoƙari ne na shigar da siyasar ubangida, da tsangwama da barazana irin na salon da ya rusa jam’iyyar PDP, wanda APC ta taso ne domin ta kawar da shi.
Idan za’a Iya tunawa tunda farko Sanata Ajibola Basiru, a matsayinsa na Sakataren Jam’iyya na Ƙasa kuma mai kula da bin ƙa’idojin APC, ya yi kira da a mutunta mukamin Gwamna tare da tabbbar da cewa kowanne gwamna shine Jagoran APC a jiharsa abinda ake ganin ya fusata Wike.
Sai dai abin takaici, acewar Hotoro a maimakon Wike ya yi martani na hankali, sai Minista Wike wanda har yanzu bai shiga APC ta hanyar doka da tsarin jam’iyya ba, kuma bako ne a gwamnatin da APC ke jagoranta ya fito da kalaman barazana da rashin ladabi.
Ya ce APC ba mallakin mutum ko rukuni ba ce Jam’iyya ce ta ƙasa baki ɗaya, mai tsari da doka.
Babu wani Minista, ko da yaushe yana ikirarin kusanci da Shugaban Ƙasa, da ke da ikon bayyana wata jiha a matsayin mallakinsa alhalin shi ba Gwamna ba ne
Sanarwar tace goyon bayan Shugaban Ƙasa ba ya nufin wuce gona da iri ba.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/fubara-ne-jagoran-apc-a-jihar-rivers-in-ji-apc-a-matakin-kasa/
“Ba za ka zama bako a gida ba, sannan ka fara yi wa mai gida barazana” In ji Muhammad Kabir Sani Hotoro
Ya kara da cewa a wannan lokaci mai matuƙar muhimmanci, wajibi ne shugabancin APC ya ɗauki mataki ba tare da jinkiri ba.
A ƙarƙashin jagorancin Shugaban Jam’iyya na Ƙasa, Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda, Kwamitin Gudanarwa na Ƙasa dole ne ya tashi tsaye ya yi Allah-wadai da wannan hali na rashin da’a da cin mutunci.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-da-apc-sun-yiwa-gwamnan-kano-yusuf-maraba-cikin-apc-sun-shirya-karbarsa-hannu-biyu-abdullahi-abbas/
Yin shiru a irin wannan yanayi ba hikima ba ne ƙarfafa rashin tarbiyya ne.
Ya zama dole Shugaban Jam’iyya ya umarci tsarin APC a Jihar Rivers da su tabbatar da cikakken biyayya ga Gwamnan Jihar Rivers, wanda a doka da tsarin jam’iyya shi ne jagoran APC a jihar.
Bugu da ƙari, wannan ɗabi’a ta barazana da raina shugabancin jam’iyya ya kamata a kai rahotonta ga Shugaban Ƙasa.
Don kare mutuncin APC da sahihancin shirin Renewed Hope, ya dace NWC ya ba da shawarar cire Nyesom Wike daga mukaminsa na Minista.
APC ba za ta ci gaba da ɗaukar bako da ke amfani da mukami wajen tsoratar da shugabancin jam’iyya ba.
Idan Minista Wike na son tasiri a APC, hanya ɗaya ce ta halal Kamar haka , ya ajiye matsayinsa na bako, ya yi rajista a matakin unguwa, sannan ya miƙa wuya ga ikon kundin tsarin jam’iyya da jagorancin Farfesa Nentawe Goshwe Yilwatda da NWC.
APC ba mafaka ba ce ga siyasar rashin da’a irin ta PDP.
Sakataren Jam’iyya na Ƙasa na da cikakken iko da nauyin doka wajen tabbatar da bin ƙa’idojin APC a kowane lungu na ƙasar nan.

