Jam’iyyar APC mai mulkin Kasa ta nemi ministan Abuja Nyesom Wike da ya ajiye mukaminsa ya mayar da hankali kan siyasar jihar Rivers idan ita yafi so.
Sakataren jam’iyyar APC na ƙasa, Ajibola Basiru, shine ya bayyana hakan inda yace a yanzu sun fahimci cewa Wike yafi sha’awar shiga hurumin da ba nasa ba fiye da abinda aka dora masa nauyi.
Basiru ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar, yana mai cewa Wike ba shi da wani hurumi ko ikon tsoma baki a harkokin jam’iyyar APC, kasancewar ba mamba ba ne a cikinta.
Wannan martani ya biyo bayan kalaman gargaɗi da Wike ya yi a lokacin wata ziyarar “godiya” da ya kai ƙaramar hukumar Oyigbo a Jihar Rivers, inda ya gargadi Basiru da ya nisanci siyasar jihar, yana mai zargin wasu na zuwa Rivers domin neman cin gajiyar kuɗaɗen jihar.
A cewar Basiru, matsayinsa na Sakataren APC na ƙasa ya ba shi damar kula da harkokin jam’iyyar a duk faɗin Najeriya, ba wai a Jihar Osun kaɗai ba kamar yadda Wike ya nuna.
KARIN LABARAI :https://tsthausa.com/fubara-ne-jagoran-apc-a-jihar-rivers-in-ji-apc-a-matakin-kasa/
“Ni ne Sakataren APC na ƙasa, kuma ayyukana ba su taƙaitu a wuri guda ba..
Saboda haka, bai dace Minista wanda ba mamba ba ne a jam’iyyar ya rika tsoma baki a harkokinmu ba,” in ji Basiru.
Ya kuma ƙaryata zargin sha’awar kuɗaɗen Naira biliyan 600 na Jihar Rivers, yana mai cewa irin wannan magana ba ta da tushe kuma ta saba wa tarihinsa na gaskiya, rikon amana da jajircewa wajen tsayawa kan gaskiya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tsarotinubu-ya-kashe-sama-da-naira-biliyan-300-don-samar-da-tauraron-dan-adam-a-abuja-inji-wike/
Basiru ya ƙara da cewa bai ji tsoron wata barazana ko gargaɗi ba, yana mai cewa gogewarsa a harkokin siyasa ta shirya shi fuskantar kowanne irin matsin lamba.
A ƙarshe, ya nanata cewa har sai Wike ya shiga jam’iyyar APC, ba shi da ikon tsoma baki ko tsokaci kan harkokin jam’iyyar a kowanne mataki.

