Kwamishinan yada labarai da Al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ya jadda cewa duk wani mai kishin Kano, to jihar ce a gabansa, a dan haka masu yaki da wannan aniya zasu Iya daura damar yakarsa.
Kwamared Waiya ya shaida hakan a yayinda yake karbar bakuncin kungiyar tsaffin Kansilolin jihar Kano da gwamnan Kano ya kammala sallamarsu hakkokinsu.
TST Hausa ta rawaito cewa tsaffin Kansilolin sun kaiwa kwamishinan ziyara ne domin nuna godiyasu da kuma bukatar Jagoran Kwankwasiyya Dr. Rabiu Musa Kwankwaso da Gwmana Abba Kabir Yusuf su jagorance su zuwa cikin APC domin cigaban Kano.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kafar-abba-kafa-ta-duk-inda-ya-shiga-ban-san-kowa-a-siyasa-ba-sai-shi-kwamared-waiya/
Kwamared Waiya ya bayyana cewa ci gaban Jihar Kano abin da ya shafi kowa ne, don haka ba za a yarda da duk wani yunkuri da zai kawo tangarda ga wannan tafiya ba.
Ya jaddada muhimmancin hadin kai, da fahimtar juna da bin hanyoyin da doka ta tanada wajen warware duk wani kalubale da ka iya tasowa, yana mai cewa cigaba na bukatar zaman lafiya da mutunta juna.
A cewarsa, duk wanda ke da ra’ayi ko shawara kan ci gaban Kano, ya kamata ya gabatar da ita ta hanyar da ta dace, domin a gina jihar cikin fahimta da jituwa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-da-apc-sun-yiwa-gwamnan-kano-yusuf-maraba-cikin-apc-sun-shirya-karbarsa-hannu-biyu-abdullahi-abbas/
Kwamishinan ya kuma yi gargadin cewa gwamnatin Kano ba zata bari a rika fadar bakaken maganganu ga Jagoran Kwankwasiyya Dr Rabiu Kwankwaso ba, yana mai cewa za’a iya daukar mataki akan ko waye.
Yace saboda irin ayyukan cigaban Kano da Gwamna Yusuf ya samar a jihar yasa kowa yake bukatarsa a siyasance.
Anasa jawabin, shugaban kungiyar tsaffin Kansilolin jihar Kano, Hon. Kata Madobi ya godewa Kwamishinan yada labarai da gwamnatin Kano akan abinda sukayi musu na fitar da hakkokinsu na tsawon shekaru da suka makale.
Kata Madobi yace babbar bukatarsu shine Kwankwaso da Abba su koma APC.

