Kwamishinan yada labarai da Al’amuran cikin gida na jihar Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya yace bai san kowa a siyasance ba sai Gwamnan Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf.
Waiya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Gwamnati da jama’a da aka gabatar a gidan Radiyon Rahma Kano.
Waiya cewa a duk inda Abba ya sanya Kafarsa, shi ma nan zai sanya tasa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/fubara-ne-jagoran-apc-a-jihar-rivers-in-ji-apc-a-matakin-kasa/
Yace babu wani ɗan siyasa da zai bi ko ya amince da shi face Abba Gida Gida kaɗai.
Ya kuma yi watsi da batun cewa Gwmana Abba ya yi butulci ga uban gidansa a siyasance wato Rabiu Musa Kwankwaso.
Waiya yace komawa APC ba yana nufin Gwamna Yusuf ya yi butulci ga Kwankwaso ba ne.
Yace asali ma Kwankwaso ne ya kafa APC a Kano a dan haka su a matsayinsu ma jikokin Kwankwaso zasu koma gidan kakansu ne.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ganduje-da-apc-sun-yiwa-gwamnan-kano-yusuf-maraba-cikin-apc-sun-shirya-karbarsa-hannu-biyu-abdullahi-abbas/
Kwamishinan yace tunda farko shugabannin kananan hukumomi da yan majalisar dokoki ne suka nemi Jagoran Kwankwasiyya da gwamna Abba su koma APC.
Kwamishina Waiya ya kuma nemi jama’a su daina yada jita jita akan abinda basu da masaniya akansa ko menene.

