Wani babban limanin Coci wato fasto Toye Ebijomore ya yi hasashen cewa Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai sanya wa Najeriya sabon suna kafin karewar wa’adin mulkinsa, tare da tsallake duk wani shiri na siyasa da ake yi domin dakile aniyar tasa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-%e2%82%a610400-kacal-ya-warewa-kowane-%c9%97an-najeriya-a-fannin-lafiyarsa-cikin-kasafin-ku%c9%97in-2026-nma/
Rahoto ya nuna cewa Faston ya bayyana hakan ne a cikin hasashensa na shekarar 2026 da ya gabatar a Akure, babban birnin Jihar Ondo.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa Fasto Toye Ebijomore ya ce hasashen ya samo asali ne daga abin da ya bayyana a matsayin bincikensa game da makomar Najeriya da siyasar ƙasar nan.
A cewar faston, za a samu gagarumin haɗin gwiwa tsakanin jam’iyyun siyasa da nufin kwace mulkin Najeriya daga hannun APC a zaɓen shekarar 2027.
Amma saidai yace shirin Tinubu na komawa mulki da sauyawa Najeriya suna zai wuce na sauran masu neman dakile shi.
Sanan yace wannan kawancen na yan hadaka ba zai daɗe ba, domin wasu masifu da rashin jituwar ra’ayi za su raunana haɗakar har ma su kai ga rugujewarsa.
Fasto Ebijomore ya ce duk da yunƙurin kawancen jam’iyyun adawa, jam’iyya mai mulki za ta iya cigaba da mulki bayan zaɓe mai zuwa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/ka-yi-hakuri-ka-yi-iya-yinka-ba-za-ka-iya-gamsar-da-kowa-ba-limamin-legas-ya-fa%c9%97a-wa-tinubu-a-hudubar-jumaa/
Ya ƙara da cewa wata sabuwar jam’iyya mai ƙarfi za ta taso a nan gaba, wacce daga bisani za ta iya ƙwace mulki daga hannun jam’iyya mai mulki a wani lokaci nan gaba.
Ya kuma roki Shugaba Tinubu da ya yi biyayya ga kiran wasu mutane ta hanyar kira a yi addu’ar ƙasa baki ɗaya domin kare martabar Najeriya.
Faston ya kuma yi hasashen cewa a shekarar 2026, Najeriya za ta shiga yanayin yalwar abinci.
Ya shawarci gwamnati da ta yi amfani da wannan dama wajen rage tsadar abinci da magunguna domin sauƙaƙa wa talakawa rayuwa.
Ya ce shekarar 2026 za ta kasance cike da yalwa da albarka, amma a lokaci guda za a fuskanci ƙarin ƙalubale da hare-hare kan mutane.

