Wasu Yan bindiga sun shiga garin Chaco da ke Ƙaramar Hukumar Wurno a Jihar Sakkwato, inda suka sace amarya da ƙawayenta 14.
Yayin da mutane ke tsaka shagalin bikin auren, sai ’yan bindigar suka afka musu tare da tarwatsa su.
Wani daga cikin iyayen ƙawayen amaryar ya shaida wa Aminiya cewa ba a tantance adadin waɗanda aka sace ba, amma wasu na cewa 15 ne, wasu kuma na cewa 13, amma amaryar da ’yarsa na cikin waɗanda aka sace.
A cewarsa, ’yan bindigar sun shiga garin ne da misalin ƙarfe 12 na daren ranar Asabar.
Sun shiga gidansu amaryar kai-tsaye inda suka yi awon gaba da ita da ƙawayenta.
Yayin da suke barin garin, matasa ’yan sa-kai sun yi ƙoƙarin dakatar da su, inda suka yi artabu, tare da yi wa ɗan ɗan sa-kai a hannu.
Ya ƙara da cewa har yanzu ’yan bindigar ba su tuntuɓi kowa ba domin neman kuɗin fansa.
Ranar Lahadi ita ce ranar da aka tsara domin ɗaura auren amaryar, sannan a kai ta gidan mijinta.
Lamarin tsaro a yankin gabashin Sakkwato na ƙara taɓarɓarewa.
Kakakin rundunar ’yan sandan Sakkwato, Ahmad Rufa’i, bai amsa kiran da aka masa ba, zuwa lokacin haɗa wannan rahoto.

