Mai Girma Gwamna,
Rufe makarantu da ake ta yi a jihohin ƙasar nan cikin su har da Kwalejojin Tarayya 47,da dukkan makarantun kwana na jihohin Katsina, Taraba, Kebbi, Niger, da sauran matakan da wasu jihohi suka ɗauka na yi daidai da matakan tsaro da muka ɗauka a Kano a watan Nuwamba 2021 Inji tsohon kwamishinan Ilimi Hon.Muhammad Sunusi Kiru.
A wancan lokaci, bayanan sirri daga hukumomin tsaro sun nuna cewa ’yan bindiga na shirin kai hare-hare a makarantu da ke kan manyan hanyoyi, waɗanda ba su da katanga, ko kuma waɗanda ke cikin yankuna masu nisa.
Karin Larabai:https://tsthausa.com/rashin-tsaro-gwamnonin-katsina-da-plateau-sun-rufe-makarantun-jihar-nan-take/
A bisa shawarar da na bayar, gwamnatin Jihar Kano ta ba da umarnin rufe wadannan makarantu na ɗan lokaci domin kare rayukan ɗalibai da malamai.
Manufar ita ce a tabbatar da tsaron dalibai da malamai yayin da ake aiki da hukumomin tsaro domin samar da tsaro.
Cikin ’yan makonni, ƙarfafa ayyukan tsaro ya tarwatsa wasu daga cikin ƙungiyoyin masu garkuwa da mutane, kuma ina yabawa hukumomin tsaro kan hulɗar kwarai da muka yi a wancan lokaci.
Da wannan daidaituwar mataki da ake samu tsakanin jihohi da gwamnatin tarayya, ya tabbatar da cewa abinda muka yi a shekarar 2021 mataki ne ingantacce, kan lokaci, kuma wanda ya taimaka wajen kare rayuka.
Duk da wadannan shaidu na gaskiya, wasu jagororin jam’iyyar NNPP sun ci gaba da kalubalantarmu da siffanta rufe makarantun da muka yi a wancan lokaci a matsayin rashin tausayi ko kokarin lalata harkar ilimi.
Karin Labarai:https://tsthausa.com/6519-2/
Wannan magana ba gaskiya ba ce, kuma tana tauye girmamawa ga iyayen da ’ya’yansu suka tsira daga hatsari ta dalilin waɗannan matakan tsaro.
Har ila yau, akwai shaidu na tabbacin cewa barazanar tsaro na ci gaba a wasu ƙananan hukumomi uku cikin 44 na Jihar Kano, lamarin da ya sake nuna gaggawar ɗaukar matakin kariya makamancin wanda aka yi a baya.
Ina fatan gwamnan Kano ba za ka bari siyasa ta rinjayi hukuncinka ba; babu wani abin kunya a kwaikwayon abin kirki da mukayi na rufe makarantun jihar Kano a wasu kananan hukumomi.
Na roƙe ka ka nuna tausayi ga ɗalibanmu na makarantun kwana, waɗanda tsaron rayukansu ya rataya a wuyan gwamnatin ka, ka kuma dauki mataki cikin gaggawa domin kare su.
Iyayen yara sun fara nuna damuwa sosai, kuma idan ba a yi bayani ko daukar mataki cikin hanzari ba, da yawa na iya janye ’ya’yansu daga makaranta da kansu.
Na fahimci cewa akwai ruɗani tsakanin bin matakan da aka tabbatar da ingancinsu ko kuma guje wa su saboda siyasa.
Ina mai roƙon ka da ka bi hanyar da ta fi dacewa ta kare rayukan yara.
Mu zabi abin da ya dace, mu kuma kare makomar ɗaliban Jihar Kano.
Naku cikin girmamawa,
Hon. Muhammad Sanusi S. Kirú, FCIA
Tsohon Kwamishinan Ilimi, Jihar Kano
24 Nuwamba 2025

