Gwamnatin Jihar Kano ta bayyana cewa ta kashe kimanin naira biliyan 928 wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa a sassa daban-daban na jihar cikin shekaru uku da suka gabata.
Kwamishinan Ma’aikatar Bibiyar Ayyukan Gwamnatin Jihar Kano, Kwamared Nura Iro Ma’aji, ne ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai na duniya da aka shirya domin bayyana irin nasarorin da gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf ta samu wajen aiwatar da ayyukan ci gaba.
A cewarsa, an kashe kuɗaɗen ne wajen aiwatar da jimillar ayyukan raya ƙasa guda 1,508, inda aka kammala 799, yayin da sauran 709 ke ci gaba da gudana a matakai daban-daban.
Ya ƙara da cewa, baya ga waɗannan ayyuka, gwamnatin jihar na aiwatar da ayyukan mazabu 619 ta hannun mambobin Majalisar Dokokin Jihar Kano a faɗin ƙananan hukumomin jihar.
Kwamared Nura Iro Ma’aji ya ce ayyukan sun haɗa da shirin farfaɗo da tsohon birnin Kano, gina titunan kilomita biyar a kowace ƙaramar hukuma daga cikin ƙananan hukumomi 38 na jihar, gina cibiyoyin ƴan sintirin tsaro a ƙananan hukumomi 36, da kuma ayyukan raya karkara da suka shafi ilimi, kiwon lafiya, samar da ababen more rayuwa da sauran shirye-shiryen inganta rayuwar al’umma.
Ya tabbatar da cewa gwamnatin Gwamna Abba Kabir Yusuf za ta ci gaba da tabbatar da inganci, gaskiya da bin ƙa’idoji wajen aiwatar da ayyukan raya ƙasa, domin tabbatar da cewa al’ummar jihar Kano sun amfana da kuɗaɗen gwamnati ta hanyar ayyukan da suka dace kuma masu ɗorewa.

