Gwamnatin jihar Kano ta nemi al’ummar jihar da su Koma ga Allah wajen dagewa da adu’oi domin kubuta daga matsalolin tsaro da ake fama da su a Arewacin Najeriya.
Gwamnatin tace lura da halin matsalolin tsaro da ake fuskanta a jiha da kasa baki ɗaya duk dacewa har Yanzu Kano da sauƙin matsalar idan aka kwatanta da sauran jihohin Arewa.
Kwamishina na biyu a hukumar shari’a ta jihar Kano Sheikh Ali Dan Abba, ne yayi wannan Kiran a wata sanarwa da jami’an hulda da jama’a na hukumar Ibrahim Ado Sabari ya fitar wacce aka rabawa manema labarai.
Yace a madadin shugaban hukumar, Sheikh Abbas Abubakar Daneji ,hukumar na nuna damuwa tare da fatan cewa matsalar zata zo karshe ba da jimawa ba.
Sheikh Ali Dan Abba ya bayyana damuwar Hukumar kan yadda ake yawaita garkuwa da mutane domin neman kudin fansa, yana mai cewa wannan dabi’a babban zalunci ne da addinin musulunci ya yi hani a kansa, kasancewar duk wani abu da ke cutar da mutane ko al’umma ba halal ba ne.
Kwamishinan ya mika sakon jajantawa ga al’ummar Karamar hukumar tsanyawa,da gwamnatin Jihar Kano, da daukacin jama’ar jiha kan lamarin sace wasu mutanen yankin da ’yan bindiga suka yi.
Ya yi addu’ar Allah Ya kubutar da su tare da kiyaye sauran jama’a daga faruwar makamancin wannan lamari.
A cewarsa, addu’a makamin musulmi ce, wadda Annabi (SAW) da Sahabbansa suka yi amfani da ita wajen tsira daga makiya.
Don haka, ya bukaci al’umma su kwantar da hankalinsu su kuma dage da addu’a domin neman daukin Allah a cikin garuruwa da makarantu da kasuwanni da sauran wuraren zaman al’umma
