Gwamnatin Jihar Kano ta amince da fitar da kudi sama da Naira miliyan 85 domin aiwatar da ayyukan samar da tsaftataccen ruwan sha a Karamar Hukumar Gwale, a wani mataki na magance matsalar karancin ruwa da al’ummar yankin ke fuskanta.
Kwamishinan yada labarai da al’amuran cikin gida na jihar Kano,Kwamared Ibrahim Abdullahi Waiya ne ya shaida halan ga manema labarai na fadar gwamnatin Kano bayan kammala zaman majalisar Zartaswa na Kano karo na 36.
Kwamared Waiya yace majalisar ta amince da gabatar da ayyukan raya kasa ciki harda biyan diya.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/kano-ta-fara-gasa-da-biranen-afurika-a-fannin-kasuwanci-da-zuba-jari-in-ji-gwamna-yusuf/
TST Hausa ta rawaito cewa zaman majalisar Zartaswar ya amince da kashe kudi sama da naira miliyan dubu 6 da miliyan dari 9 domin gudunar da ayyukan raya kasa a jihar.
A cewarsa bayanan samar da ruwa a wasu Wuraren gwamnati, zata inganta kayayyakin aikin samar da ruwan sha, domin tabbatar da wadatar ruwa mai tsafta ga mazauna yankin Gwale.
Sai kuma karkatar da hankali wajen inganta Muhalli da noma da saurnasu.
KARIN LABARI:
Daga nan ya tabbartar dacewa wannan shiri na daga cikin manufofin gwamnati na bunkasa kayayyakin more rayuwa, musamman a bangaren ruwa da tsafta, wadanda ke da matukar muhimmanci ga lafiyar al’umma da cigaban tattalin arziki.
Waiya ya kuma ce gwamnatin zata jayo hannun masu zuba jari a jihar ta Kano a wani mataki na inganta Tattalin Arzikin jihar.
Sannan kwamishina Ibrahim Abdullahi Waiya yace majalisar Zartaswa ta amince da fitar da kudi sama da naira miliyan dari 8 da 59 domin biyan diya ga wadanda ayyukan kilomita biyar biyar na kananan hukumomi

