Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya yi alkawarin sake baiwa yan fanshon Kano hakokinnsu karo na uku a jihar Kano,ranar Alhamis 9 ga watan Janairun 2025.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da hakan ne a yayinda yake kaddamar da sake baiwa matan Kano 5,200 kudi naira dubu 5 kowaccensu daga kananan hukumomi 44 na jihar.
Gwamna Yusuf ya ce a wannan rana ta Alhamis gwamnatinsa zata sake baiwa yan fanshon hakokinnsu ne domin inganta walwalarsu a jihar kano.
Duk dacewa, gwamna Yusuf bai sanar da nawa zai sake saki karo na uku ga yan fanshon ba amma yace , gwamnatinsa ba zata yi watsi da rayuwarsu ba.
A ranar 3 ga watan Disamba na shekarar 2023 ,gwamna Yusuf ya amince da sakin naira biliyan 5 domin sallamar yan fanshon a karon farko.
Inda Kuma a ranar 8 ga watan Mayun 2024 a karo na biyu , gwamna Yusuf ya sake amincewa da sakin naira biliyan 6 domin sallamar yan Fansho su a kalla 6,000 da suka yi ritaya daga shekarar 2016 zuwa 2019 da ba’a basu hakokinnsu ba.
Gwamna Yusuf ya ce a wannan lokaci na tsadar rayuwa,yasan dole yan Fanshon da ba’a sallama ba ,suna cikin wani hali na kuncin rayuwa.

