Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya tabbatar da aniyarsa na inganta walwalar ayyukan manema labarai a Kano.
Gwamna Yusuf ya tabbatar da hakan ne bayan kammala Saka hannu a kasafin kudin shekarar 2025 a fadar gwamnatin Kano.
Gwamnan yace yayi shiri na musamman a cikin kasafin kudin shekarar ta 2025 Kuma daga cikin mutanan da zai sakawa da Alkairi harda manema labarai.
A wata sanarwa da Daraktan yada labarai na gwamnan Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace gwamna Yusuf duk da bai shaida irin abubuwan da zai sakawa yan jarida dasu ba ,amma yace yana sane da gudunmowar da suke bashi
Ya tabbatar dacewa irin kokarin da manema labarai suke yi wajen ganin tafiyar da gwamnatinsa yadda ya kamata ba zai tafi a banza ba .
Ya yaba musu tare da bukatar da su cigaba da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu.
Bayan yabawa Yan majalisar dokokin kano akan hadin kan da suke bashi musamman yadda a cikin dan lokaci suka amince da kasafin ,yace kusan irin wannan gudun mowar manema labarai suke bashi a Kano.
Ya kuma taya al’umar Kano murnar samun kasafin kudin cikin nasara tare da tayasu murnar shiga sabuwar shekarar 2025.

