Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya nemi amincewar Majalisar Dattawa domin karɓo sabon bashin ƙasashen waje da ya kai dala biliyan 20.5 da kuma yuro biliyan 1.04.
TST Hausa ta rawaito cewa kwatankwacin kudin a Naira sun tasamma sama da naira Tiriliyan 31.
Wannan buƙata na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da muhawara kan yadda ƙasar nan za ta tafiyar da basussukanta da kuma biyan kuɗaɗen da take bin masu ba ta rance.
Sai dai ana buƙatar ƙarin bayani kan sharuɗɗan bashin, lokacin da za a fara biya da kuma takamaiman ayyukan da za a kashe kuɗaɗen a kansu.

