Wani sabon bincike da babban bankin Switzerland UBS ya gudanar ya gano cewa, an samu ƙaruwar attajirai a duniya a shekarar 2025 da ake bankwana da ita, wanda hakan na da nasaba ne da ƙaruwar farashin kayayyakin da kamfanonin fasaha ke fitarwa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/rage-farashin-fetur-da-mukayi-shine-dalilin-sauke-farashin-a-najeriya-ba-janye-harajin-kaso-15-ba-matatar-dangote/
A cewar rahoton da aka fitar cikin watan nan na Disamba kimanin attajirai 2,919 ake da su yanzu haka a duniya, wanda hakan ke nuna cewa an samu ƙaruwar sama da 200 idan aka kwatanta da adadin 2,700 da aka gani a shekarar da ta gabata.
Binciken ya ƙiyasta cewa, jimillar dukiyar waɗannan attajiran ta kai dala tiriliyan 15.8.
A cewar rahoton, wannan ƙari da aka samu, ya samo asali ne sakamakon hauhawar farashin kaya da aka samu daga kamfanonin fasaha.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/dangote-ya-sauke-kansa-daga-jagorancin-kamfaninsa-ya-na%c9%97a-magajinsa-bayan-shekara-20-yana-shugabanci/
Amma rahoton ya ci gaba da cewa, akwai mutane da suka zama attajiranta hanyar gado, daga ɗimbin dukiyar da iyayensu suka mutu suka bari.
A Amurka, yanzu haka akwai attajirai 924, in ji bankin UBS, waɗanda ke da kimanin dala tiriliyan 6.9.
Haka zalika cikin sabbin attajirai 196 da aka samu, 87 sun fito ne daga Amurka.

