Kwamishinan harkokin sufuri na jihar Kano, Ibrahim Ali Namadi Dala , ya nesanta kansa daga Sulaiman Danwawu, wanda ake zargi da laifin fataucin miyagun kwayoyi kuma yana fuskantar shari’a a kotun tarayya da ke Kano.
Jaridar DAILY NIGERIAN ta rawaito cewa Kwamishina Namadi ya tsaya wa Danwawu beli a gaban kotu, lamarin da ya janyo ce-ce-ku-ce a ciki da wajen Kano.
Sai dai a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau Juma’a, Kwamishina Namadi ya bayyana cewa bai da wata alaka ta kusa ko ta nesa da wanda ake zargi, dan kwaya ne kuma ya amince ya tsaya masa ne kawai bayan wasu manyan mutane masu daraja da amana sun nemi alfarma tare da shaidar da kyawawan halayensa ashe bai san yaudararsa akayi ba , acewarsa.
TST Hausa ta rawaito cewa alkalin kotun, mai Shari’a M.S. Shuaibu, ya bayar da belin wanda ake zargin ne bayan sauraron rokon lauyoyinsa a ranar 17 ga Yuli,” in ji shi.
Sanarwar tace bayar da beli a irin wannan shari’a abu ne da ya dace da tsarin doka, domin wanda ake tuhuma ana kallonsa a matsayin mara laifi har sai an tabbatar da laifinsa a kotu.
Namadi ya ce wani bangare na sharuddan belin ya bukaci a samu wanda zai tsaya wa wanda ake zargi daga cikin kwamishinonin gwamnatin Kano, kuma wasu mutane da ya yarda da su suka roki da ya tsaya masa, lamarin da ya ce ya amince da shi da zuciya daya.
“Ban taba sanin girman laifukan da ake zarginsa da su ba, kuma bayanan da suka fito a baya-bayan nan sun girgiza ni matuka,” in ji Kwamishinan.
Ya yaba da kokarin Gwamnatin Jihar Kano wajen yaki da shaye-shaye da miyagun kwayoyi, da kuma kokarin da ake yi wajen gyara rayuwar matasa da suka fada tarkon amfani da kwayoyi.
“Abubuwan da nake darajantawa a rayuwa ba su da nasaba da goyon bayan masu aikata laifi ko bijirewa dokokin kasa,” in ji shi.
Namadi ya ce ya riga ya nemi shawarar lauyoyinsa domin sanin matakin da ya kamata ya dauka a gaba, ciki har da yiwuwar janye tsayuwar belin da yayi.
“Ina matukar nadamar shiga wannan lamari da bai dace ba, kuma ina tabbatar wa da gwamnatin Jihar Kano da al’ummarta cewa ina nan daram wajen kare gaskiya, adalci da bin doka da oda.”
Ya kuma jaddada cewa ba zai taba mara wa wani baya da zai kawo cikas ga yaki da safarar miyagun kwayoyi da ta’addanci da sauran munanan dabi’u da ke barazana ga zaman lafiya da ci gaban jihar ba.

