Kamfanin man fetur na Najeriya NNPCL ya umarci gidajen man fetur na Najeriya mallakinsa su gaggauta rage farashin litar mai ba tare da bata lokaci ba.
Kamfanin na NNPCL duk da cewa bai fadi dalilin hakan ba ,Amma ya tura wannan sanarwa ne ga Shugabannin shiya shiya na Najeriya.
A wani sakon murya da Eng Nuraddeen Aliyu Wanda daya ne daga cikin cikin manyan dilolin dakon man fetur kuma mai kula da gidan man fetur na NNPC dake tashar mota ta Kano Line ,ya aikewa Jaridar TST Hausa,yace an tura musu sakon cewa su sauke farashin litar mai a Jigawa da Kano Kuma ga sabon farashin da zasu koma amfani dashi nan ,kamar yadda sanarwar ta nuna.
Yace a Jigawa an basu umarnin su sayar da fetur akan naira 975 sai Kuma Kano su sayar akan naira 965.
Wannan na zuwa ne Kwanaki kadan bayan da aka sanar da kara kudin man fetur a Najeriya zuwa naira dubu 1 da dari daya a hamsin zuwa naira dubu daya da naira hamsin.

