Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya jagoranci rantsar da sabbin kwamishinoni guda bakwai da ya nada a watan Disambar 2024 da ya gabata.
Kwamishinan shari’a na Kano Kuma babban lauyan jihar, Barista Haruna Isa Dederi shine ya rantsar da sabbin kwamishinonin 7 tare da sauran masu baiwa gwamna shawara.
Bugu da kari gwamnan ya jagoranci rantsar da sabbin manyan sakatarorin gwamnati guda 6 (Permanent secretaries) da aka daga likkafarsu zuwa mataki na gaba a aikin gwamnati.
Haka kuma gwamna Yusuf ya jagoranci rantsar da masu bashi shawara guda 13 daga cikin guda 15 da aka nada.
TST Hausa ta rawaito cewa tuni gwamna Yusuf ya tura sabbin kwamishinonin zuwa ma’aikatun da aka tanadar musu.
Gwamnan ya amince da hakan ne a fadar gwamnatin jihar Kano ranar litinin 6 ga watan Janairun shekarar 2025.
Sabbin Kwamishinonin da gwamna Yusuf ya jagoranci rantsarwa kuma ya amince da basu ma’aikatun da zasu jagoranta sun hada da :
1.Alhaji Shehu Wada Sagagi, da zai kula da ma’aikatar kasuwanci da zuba jari ta kano
2.Kwamared Ibrahim Abdullahi Waya, an turashi ma’aikatar kula da yada Labarai ta Kano
3.Dr.Dahir Muhammad Hashim an amince ya rike ma’aikatar kula da Muhalli ta kano
4.Abdulkadir Abdussalam, gwamna ya amince ya rike ma’aikatar kula da Raya karkara ta Kano
5.Dr. Isma’ila Aliyu Dan Maraya ,an turashi ma’aikatar kula da Kudi ta Kano.
6.Dr.Gaddafi Sani Yakubu ,an turashi ma’aikatar Kula da makamashi ta Kano
7.Dr.Nura Iro Ma’aji , ma’aikatar gwamna Abba ya amince ya rike ma’aikatar Kula da yadda bada kwangiloli da bibiyar ayyukan gwamnati
Gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ce ya dauki matakin samar da sabbin kwamishinonin ne domin inganta ayyukan gwamnati da Kuma kawo cigaba a Kano.
Sabbin Kwamishinonin zasu fara zaman majalisar zartaswa na nan gaba da za’a sanar.
TST Hausa ta gano cewa a ranar Talata 18 ga watan Disamba na shekarar 2024 data gabata ne majalisar dokokin Kano ta amince da mutane 7 din da gwamna Abba Yusuf ya tura mata dan a tantancesu a kuma amince masa ya nada su kwamishinoni,bayan garambawul da yayi a cikin majalisar zartaswarsa.
Gwamna Yusuf ya taya kwamishinonin murna tare bukatarsu da su jajirce wajen gudanar da ayyukansu yadda ya kamata, tare da rungumar kowa a gwamnati dan amfana da romon Demokaradiyya.
Gwamnan ya kuma nemi sabbin kwamishinonin da masu bashi sharawa da su rike gaskiya da amana yana mai shaida cewa rantsuwar da sukayi na yiwa jama’a aiki ,rantsuwa ce ta kare muradun mutanan kano.

