Fadar shugaban kasa ta yi watsi da jita-jitar da ake yadawa game da sauke shugaban hukumar zabe ta kasa (INEC), Farfesa Mahmud Yakubu tare da maye gurbinsa da wani Bayarabe
TST Hausa t rawaito cewa an ta yawo da Wani sako da aka yada a kafar sadarwa ta WhatsApp da ya nuna cewa an kori Farfesa Mahmud wanda aka yada cewa an maye gurbinsa da Farfesa Bashiru Olamilekan.
Farfesa Olamilekan ya fito ne daga jihar Ogun.
Fadar ta Shugaban kasa ta bayyana labarin a matsayin kanzon kurege.
A wata sanarwa da babban mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin kafafen sadarwa na zamani, O’tega Ogra ya fitar, ya bukaci jama’a da su yi watsi da irin wadannan labarai na jita-jita.
Yace an yada labarin ne domin kokarin tunzura jama’a.
Ya bayyana cewa duk wata sanarwa a hukumance game da matsayin shugaban hukumar zabe ta kasa INEC zata fito ne daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya ko wasu hukumomi da aka baiwa izini.
Fadar tace har yanzu Farfesa Mahmud Yakubu ne Shugaban INEC.

