Kwamishinan kula da harkokin tsaro da al’amuran cikin gida Manjo Janaral Muhammad Inuwa Idiris mai ritaya ya ajiye aikinsa.
A Wata takarda da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya fitar yace gwamna Yusuf ya kadu da ajiye aikin da kwamishinan yayi
Ya kuma mika sakon godiya sosai abisa gudun mowar da ya bayar.
Tuni gwamna Yusuf ya karbi takardar ajiye aikin na kwamishinan tsaron nan take.
TST Hausa ta rawaito cewa kwamishinan bai bayyana dalilansa na ajiye aikin ba.
A ranar 16 ga watan Augusta na shekarar 2024 , gwamna Yusuf ya rantsar da Manjo Janaral Muhammad inuwa a matsayin kwamishinan tsaro na cikin gida bayan mako daya da nadinsa domin kawo karshen fadace fadacen daba da sauran matsalolin tsaro a kano.

