Kungiyar Kwadago ta Najeriya NLC ta sanar da 4 ga Fabarerun 2025, a matsayin ranar da zata fara zanga zangar gama gari a Najeriya domin nuna fushinta akan karin kuɗin kiran waya da na Data da kaso 50 cikin 100.
Kungiyar ta NLC ta sanar da matsayar ne a wata sanarwa data fitar a Abuja a dazu da yamma bayan kammala taronta na majalisar zartaswa.
A ranar 22 ga watan Janairun shekarar 2025 NLC tayi watsi da karin kuɗin kiran waya da Data da Kamfanonin sadarwa suka Yi.
Wannan na zuwa ne bayan da Hukumar Sadarwa ta Najeriya NCC a ranar 20 ga watan Janairu, 2025, ta sanar da amincewarta ga kamfanonin sadarwa su kara kuɗin kiran waya da na Data ga yan Najeriya da kashi 50 cikin dari.
Amincewar dai ya janyo cece kuce tsakanin yan kasa da ita kanta Kungiyar ta Kwadago Inda ta yi watsi da karin kuma tayi barazanar shiga zanga-zanga da kauracewa amfani da hanyoyin sadarwa na Kamfanoni muddin ba’a koma yadda ake a baya ba.
NLC tace Zanga-zangar na a matsayin gargadi ne ga gwamnati cewa ma’aikata sun bijirewa karin kuɗin kiran waya da na Data saboda hakan zai kara ta’azzara talauci a fadin kasa.
TST Hausa ta rawaito cewa da yiyuwa gwamnatin tarayya ta magantu kan hakan anan gaba.

