Yan sanda sun kama tsohon shugaban hukumar yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano (PCACC),Barista Muhuyi Magaji Rimingado, a wani samame da ya ja hankalin jama’a saboda yadda aka gudanar da shi, lamarin da ya haifar da cece-kuce
Rahotanni sun bayyana cewa tawagar ’yan sanda daga Abuja ta isa Zaria, inda Rimingado yake ganawa da lauyansa, sannan ta kama shi ba tare da nuna takardar kama ba, a cewar shaidun da ke wurin.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/shinkafar-tinubu-da-muka-kama-a-kano-ta-kai-naira-biliyan-1-inji-muhyi/
Ganau sun ce jami’an sun je Zaria me cikin motocin da suka cika da makamai, kuma sun yi barazanar ɗaukar mataki kan duk wanda ya yi ƙoƙarin tsoma baki.
Wani ganau ya ruwaito cewa, “Sun shiga garin ne cikin hanzari, kuma sun ce daga hedkwatar ’yan sanda a Abuja suke.
Saidai TST Hausa ta rawaito babu wanda ya nuna wata takarda kafin su kama shi.
Kamen na zuwa ne bayan dogon rikici tsakanin hukumar PCACC a lokacin jagorancin Rimingado da wasu manyan jami’an gwamnati, musamman kan binciken da hukumar ta gudanar game da zargin karkatar da dukiya da kadarori da suka shafi tsohon daraktan Kamfanin taki na KASCO.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/mahimman-mutane-dake-bukatar-tsaro-za-su-koma-amfani-da-yan-civil-defense-maimakon-yan-sanda-in-ji-tinubu/
Wannan bincike ya hasko zargin karkatar da sama da Naira biliyan 4, lamarin da ya jawo takaddama tsakanin hukumar da wasu hukumomi na tsaro.
A baya, wata kotu ta bayar da umurnin hana ’yan sanda kama Rimingado har sai an kammala shari’ar da ya shigar, amma hakan bai hana sake kamun a jiya ba.

