Fadar shugaban kasa tayi watsi cece kucen wasu bangarori keyi akan sabuwar dokar Haraji ta 2024.
Babban mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Temitope Ajayi, a wani rubutu da ya wallafa a shafinsa na X yace sauye-sauyen ya samo asali ne sakamakon gudummawar da kwararru sama da 80 suka bayar a tsawon watanni 14 da suka shafe suna nazari.
Fadar ta shugaban kasa tayi gargadin cewa duk wani jinkirin da aka samu wajen kin amincewa da wannan doka to fah sai an kwashe shekaru 20 ba’a dawo daidai ba.
A cewar Ajayi, jin gine sauye-sauyen harajin zai zama babban kuskure da al’ummar kasar ba za su iya biya ba.
Yace wadanda suke adawa da dokar basu gama saninta ba kuma ba masana ba ne .
Idan ba’a manta ba Gwamnan Jihar Borno, Babagana Zulum, ya yi gargadin cewa kudirin na iya yin illa ga yankin Arewa da sauran sassan Najeriya.
A wata hira da BBC Hausa a ranar Juma’a, Zulum ya soki yadda kudirin ke tafiya cikin sauri ta hanyar aiwatar da dokae, inda ya kwatanta da kudurin dokar masana’antar man fetur, wanda ya dauki tsawon lokaci sabanin wannan dokar ta haraji

