Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta ce akalla ‘yan Najeriya miliyan 14 ne ke shan miyagun kwayoyi ko Kuma a kirasu yan kwaya.
Mataimakiyar kwamandan hukumar ta NDLEA ta jihar Ondo, Mrs Yetunde Joyifous, ta bayyana hakan a wani shirin wayar da kan jama’a game da illolin shaye-shayen miyagun kwayoyi wanda Kungiyar Matasan Oijefon na Makarantun Sakandire da ke Ile Oluji/Oke-Igbo a Karamar Hukumar Oke-Igbo ta Jihar ta shirya.
Joyifous ta ce, magungunan da ake amfani da su galibi sinadarai ne dake saurin sauya tunanin masu amfani da su.
A cewarta, hanya daya tilo da za a iya dakile wannan mummunar dabi’ar ta shan miyagun kwayoyi da babu babba babu yaro sun hadar da gudunmowar dukkan masu ruwa da tsaki a cikin al’umma tare da karfafa guiwa ga hukumomin da abin ya shafa wajen yaki da shan miyagun kwayoyin.
Ta bayyana matasa musamman wadanda ke matakin makarantun Sakandare a matsayin wadanda suka fi fama da wannan matsalar shaye-shayen miyagun kwayoyin a Najeriya, inda ta kara da cewa dole ne a kara kaimi wajen ganin an ceto daliban daga halin da suke ciki.
Tace da yawa daga cikin hukumomin makarantun sakandire da iyayensu a Najeriya basa iya gano yadda daliban ke amfani da miyagun kwayoyin masu sa maye ba a makaranta ko wajenta.
A jawabinsa na maraba,tunda farko shugaban kungiyar matasan Oijefon, Adedokun Adeyonu, ya ce majalisar matasan ta shirya shirin wayar da kan matasa ne domin ceto su daga kan karkatacciyar hanyar da suke kai.
Adeyonu ya kuma bayyana tasirin abokai, da kuma kallon wasannin kwaikwayo da sauraron kade-kade, a matsayin abubuwan da ke jefa matasa cikin shaye-shayen miyagun kwayoyi.

