Tsohon gwamnan jihar Kogi, Alhaji Yahaya Bello, ya ƙara aure inda ya auro matarsa ta huɗu mai suna Hiqma a wani biki na sirri da aka gudanar a ranar Asabar da ta gabata a birnin Abuja.
TST Hausa ta rawaito cewa,iya makusantan Yahaya Bello da na jikin amarya ne kadai suka halarci bikin auren.
Wannan sabon aure ya fito fili ne bayan matarsa ta uku, Hafiza Bello, ta bayyana hakan a shafinta na Instagram abinda ya janyo cece kuce
A cikin wani faifan bidiyo da ta wallafa daga bikin, Hafiza ta nuna godiyarta ga Allah tare da yi wa sabuwar amarya maraba cikin iyalinsu.
“Tace Allahamdulillah yanzu iyalanmu sun karu zuwa hudu,Muna yiwa amarya sannu da zuwa ”
A cewar rahoton DAILY POST, kafin wannan aure, Yahaya Bello na da mata uku da suka hada da Amina Oyiza Bello,da Rashida Bello, da Kuma Hafiza Bello.

