Mai gabatar da kara na hudu a shari’ar da ake yi wa tsohon gwamnan jihar Kogi da ake zarginsa da karkatar da kudade, ya karyata, da kakkausan kalaman da lauyan hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, na cewa wasu jami’an tsaron tsohon gwamnan suna tursasa shi ya bayyana wasu kalamai a gaban kotu.
Mshelia Arhyel Bata, jami’in bankin Zenith, ya ce, a karshen tambayoyin da aka yi ranar Juma’a, ya ga ya kamata ya yi karin haske kan zargin da Kemi Pinheiro, SAN ta gabatar a farkon zaman ranar.
“Mai shari’a ina so in yi karin haske game da batun da aka gabatar a baya kafin a fara shari’ar, ba wani bayanin tsaro da aka yi ma wanda ake karar cewa ya tursasa ni. “Ba a tursasa ni ko kadan ba, kuma na ga ya kamata in bayyana hakan,,” in ji shi.
Lauyan wanda ake kara, Joseph Daudu, SAN, ya kuma bukaci Alkalin kan wani labari a shafin hukumar EFCC, inda ya ce an tursasa shedunsu.
Ya kuma ce hukumar ta EFCC ta bata bayanan gaskiyar shari’ar da aka yi a ranar da ta gabata.
Da yake mayar da martani, Pinheiro, SAN ya ce zai ja kunnen ofishin EFCC kan lamarin.
Shaidan, a yayin amsa tambayoyi da Joseph Daudu, SAN, Lauyan wanda ake kara ya yi, ya kuma tabbatar da cewa tsohon gwamnan ba shi ne mai sa hannu ko alaka da duk wani asusun da aka gabatar a matsayin shaida ba.
Ya yarda cewa, takardun 22A, daga shafi na 24 zuwa 413, ba a sanya Yahaya Bello a cikin kowane takarda a matsayin wanda zai ci gajiyar duk wani aiki da aka yi ba.
Jami’in ya bayyana sunayen wadanda suka rattaba hannu a asusun gwamnatin jihar Kogi a baya, sannan kuma ya tabbatar da takardun da suka gabatar da wadanda suka maye gurbin wasu manyan jami’an gwamnatin.

