Shugaban rundunar yan kishin Kano(Kano patriotic front),Manjo Janar Ibrahim Sani Yakasai mai ritaya yayi barazanar kama sunayen mutane biyar da ake zargin cewa sune suke daukar nauyin ayyukan yan Daba a Kano.
Ibrahim Yakasai ya shaida hakan ne a lokacin da yake jagorantar zaman sulhu tsakanin jagororin yan dabar Kano da kuma kwamitocin tsaro na unguwanni a kalla 20 a ofishinsa.
Shugaban,yace babu wani dalili da zaisa ,wasu yan tsiraru su hana mutane sallar Asuba ,ko fita a lokacin da suke so , musamman cikin dare.
TST Hausa ta rawaito cewa duk da jagororin yan dabar basu halarci taron ba,amma Manjo Janar Ibrahim Sani Yakasai mai ritaya yace a shirye suke su kama sunayen manyan mutane guda biyar da ake zargin sune suke daukar nauyin hana Kano ta zauna lafiya.
Yace a zama na farko wasu daga cikin yan dabar ne suka shaida musu masu daukar nauyin ayyukansu ,sai Kuma bincikensu ya gano musu.
Sannan ya tabbatar dacewa duk wani dan Daba da ya shirya tuba kuma zai ajiye makamansa ,zasu bashi aikinyi ko Sana’a.
Yakasai ya kuma zargi wasu jami’an tsaro musamman yan sanda da zuba idanu a wasu lokatan ana fadan daba a cikin birnin Kano.
Mutane biyar din da ba’a bayyana sunansu ba ,an gano cewa uku daga cikinsu sun fito ne daga yankin Kano ta Arewa sai mutum daya da yake rike da babbar kujerar sarauta a Kano,yayinda na biyar ya taba rike kujerar Shugaban karamar hukuma a cikin birnin Kano.
Manjor Janar Ibrahim Sani Yakasai ya tabbatar da cewa nan gaba zasu kama sunayen mutanen dake daukar nauyin hana Kano zama lafiya a kafafen yada labarai, muddin basu daina ba.

