Babban akanta Janar na jihar Kano wanda kuma aka tantance a matsayin kwamishina Abdulkadir Abdussalam ya nemi Malaman makaranta a kano musamman na Furamare suyi hakuri saboda jinkirin biyan albashin watan Nuwanba da ya gabata.
Abdulkadir Abdussalam ya bayyana hakan ne a wata hira da manema labarai a ofishinsa kan matsayin da ya Samu na zama kwamishina.
Yace har yanzu akwai ma’aikatan kano da ba’a tantancesu ba dan tabbatar da sahiha cinsu.
Amma yace an karawa ma’aikatan wa’adi na karshe zuwa karshen watan Disamba na shekarar 2024.
Ya kara dacewa wanda ba’a tantance ba kafin watan Janairun shekarar 2025 to ya dauki kansa a matsayin korarren ma’aikaci.
Gama da jinkirin da aka samu wajen biyan Malaman makaranta na Furamare da sakandire da sauran ma’aikatan da basu ga albashinsu na watan Nuwanba ba ,Akanta Janar yace hakan ya samo asali ne saboda sauya bankuna da gwamnatin Kano tayi da Kuma aikin sauye sauyen shigar da mafi karancin albashi da gwamnan Kano yace zai fara biya a watan Nuwanba.
Yace ofishinsa na sane da Wanda har yanzu basu ga albashinsu na watan Nuwanba ba .
Ya kuma godewa gwamnan kano abisa nadin da yayi masa na kwamishina Ylyana mai cewa a ahirye yake ya hada kai da duk masu ruwa da tsaki wajen ciyar da Kano gaba a bangaren tattalin arziki da kudaden shiga

