Tsohon Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya rasu a Asibiti a London bayan gajeruwar rashin lafiya.
Tsohon hadiminsa akan kafofin yada labarai Bashir Ahamad shine ya sanar da hakan a shafinsa na sada zumunta Inda yace iyalansa ne suka sanar da mutuwar sa.
Ya rasu yana da shekaru 82 da haihuwa a duniya.
An haifeshi a ranar 17 ga watan Disamba na shekarar 1942 ya koma ga Allah ranar 13 ga watan Yuli na 2025.
Ya mulki Najeriya a zamanin mulkin soja daga shekarar 1983 zuwa 1985.
Daga nan ya koma mulkin farar hula a shekarar 2015 zuwa 2023.

