Gamayyar kungiyoyin tsoffin dalibai na Makarantun dake karkashin Gidauniyar Musulunci ta Abdullahi Mai Masallaci sun kashe kudi kimanin Naira miliyan daya da rabi wajen gudanar da ayyukan inganta harkokin koyo da koyarwa a makarantun.
Ayyukan sun hadar da daga darajar dakin gwaje-gwaje da bincike na Makarantar ta yadda dalibai dake rubuta Jarabawar kammala sikandire ta WAEC da NECO za su iya amfani da shi a yayin Jarabawar gwaji ta darussan Kimiyya.
Da yake jawabi a yayin taron kaddamar da Dakin gwaje-gwajen da aka daga likafarsa, shugaban gamayyar kungiyoyin daliban na makaratun dake karkashin Gidauniyar Abdullahi Mai Masallaci, shugaban kungiyar, Comrade Muhd Nura Yusuf, ya ce baya ga daga darajar dakin gwaje-gwajen, suna kuma kan gudanar da ayyukan gyare-gyare a dukkan makarantu uku dake karkashin Gidauniyar.
Haka kuma sun bayar da tallafin kudi Naira miliyan daya ga Gidauniyar do tallafawa ga aikin gina shaguna da take yi da nufin samarwa da makarantun karin hanyoyin samun kudin shiga…
Comrade Muhd Nura Yusuf ya yi kira ga sauran tsofaffin daliban rukunin makarantun dama sauran jama’a su shigo domin bada tasu gudunmawar kasancewar hakan aiki ne na sadaka jariya.
A jawabinsa, shugaban makarantar bangaren sikandire, Malam Abubakar Ibrahim bayyana jin dadi yayi tare da godewa gamayyar kungiyoyin daliban makarantun bisa gudunmawar da suke baiwa tsohuwarr makarantar tasu…
A nasa bangaren, Malam Isah Shehu Ringim wanda ya wakilci shugaban kungiyar iyaye da makamai ta rukunin makarantun, Sheikh Ahmad Tijjani Mai Salati Indabawa, ya tabo tarihin yadda a baya komai ake ba da shi kyauta a makarantar.
Ya ce sai dai a halin yanzu yanayi ya sauya don haka akwai bukatar iyayen yara su tashi tsaye, kamar yadda makarantar ta fadada harkokin koyarwa a cikinta….

