Rahotanni na nuni da cewa wata Uwar Marayu Malama Saratu Yusuf ta tare a kangon tsohon ofishin hukumar kula da jarabawar kammala sakandire ta kasa JAMB shiryar Kano saboda tsadar rayuwa bayan korarta daga gidan haya.
TST Hausa ta rawaito cewa Malama Saratu da take zaune da mai gidanta a unguwar Gandun Albasa ,an koreta daga gidan haya ne bayan mutuwar mai gidanta a watan Oktoba da ya gabata.
Daga nan bayan korarta Kuma ta rasa Inda zata zauna kasancewar bata da kowa a Kano in banda mai gidanta,sai wani magidanci ya tausaya mata bayan ya ganta a kan titi ita da yayanta ,ya nuna mata tsohon ofishin hukumar ta JAMB daga nan ta fara kwana a ciki .
Matar mai Yaya kusan uku harda kanana tana fama da kalubalen rayuwa ciki harda rashin abinci da hunturin sanyi dake damunta.
Rahotanni da TST Hausa ta samu na nuni dacewa ,bayan fara zamanta a kangon tsohon ofishin hukumar ta JAMB,sai wasu jami’an gwamnati suka yi mata gargadin cewa ta fara shirin barin wajen a kowanne lokaci .
A yayinda take zantawa da TST Hausa, Malama Saratu Yusuf tace sukan shafe kwana biyu a jere basuci abinci ba .
Cire tallafin Man fetur da Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu yayi a ranar 29 ga watan Mayun 2023 da Kuma wasu tsare tsaren gyaran tattalin arziki kasa da ya billo dasu na daga cikin dalilan da suka jefa yawancin yan Najeriya cikin mawuyacin hali.
Saidai Bola Tinubun ya nanata cewa sai nan gana yan Najeriya zasu ga ribar matakan da ya dauka na sauye sauyen gyara tattalin arziki.
A jihohin Arewacin Najeriya,mutane da dama sun koma kwanan kango ko kasan gada wasu Kuma sun koma karkara daga birane saboda tsadar gidajen haya bayan kare Karen kudade da masu gidajen sukayi .
Idan ba’a manta ba a makon da ya gabata ne Kungiyar Malaman jami’oi ta kasa ASUU ta nuna damuwa bayan samun rahoton yadda wasu malamai suka koma kwana a ofisoshinsu saboda tsadar man fetur da tsadar rayuwa
Yanzu dai Saratu Yusuf bata san makomarta ba ,Koda yake ta nemi jama’a su tayata adu’a

