Kungiyar yan kishin Najeriya tayi Allah wadarai da karuwar matsalolin tsaro da tabarbarewar tattalin arziki a Najeriya musamman Arewa.
Kungiyar kuma ta nuna damuwa akan yadda ake keta hakkin dan Adam musamman a Arewa.
Shugaban Kungiyar na Najeriya Kwamared Abdulmajid Yakubu Dauda ya bayyana hakan a wani taron manema labarai da Kungiyar ta kira a Kano.
Haka kuma Yakubu Dauda ya nuna damuwa akan halin kunci da al’umar Arewa ke ciki.
Kungiyar ta yan kishin Najeriya ta nemi Shugaban kasa Bola Tinubu da ya sauya dabarun da yake dauka na yiwa tattalin arziki garambawul.
Kwamared Yakubu Dauda ya nuna bacin ransa saboda yadda Shugaban kasa Bola Tinubu baya jin koken talakawan kasa kan halin da suke ciki yana mai cewa babu abinda zai hana yan kasa neman hakkinsu na samun walwala mutukar Bola Ahmad Tinubu bai sauya ba ,tunda yan kasa ba bayi ba ne da ake bautar da su.
“Ba’a taba yin Shugaban da yake kin sauraren jama’arsa sama da Tinubu ba a tarihin Najeriya,inji Dauda.
TST Hausa ta rawaito cewa, Kungiyar ta shaidawa manema labarai cewar mutukar , Tinubu ya ci gaba da kin sauraren jama’arsa,to zasu sake fitowa zanga-zangar irin wacce akayi a watan Augusta na 2024.
A karshe Kungiyar ta nemi Shugaba Tinubu ya sauya dabarar da ya dauka na farfado da tattalin arzikin Najeriya ta hanyar dawo da tallafin man fetur da inganta tsaro da wutar lantarki,da bude iyakokin Najeriya ,kafin nan da lokacin da suka debarwa kansu na fara zanga-zangar ya cika.
A ranar 1 ga watan Augusta na shekarar 2024 ne ,yan Najeriya suka fita zanga-zangar tsadar rayuwa da Kuma kyamar gwamnatin Tinubu,Inda suke bukatar samar da kyakyawan Shugabanci

