Shugaba Bola Tinubu zai gabatar da kasafin kuɗin shekarar 2026 a zaman haɗin gwiwa na majalisar Tarayya a gobe Juma’a 19 ga watan Disamba da misalin ƙarfe 2 na rana.
Rabotanni na cewa za a tsaurara tsaro a harabar majalisar, kuma duk waɗanda ke da aiki a majalisar dole ne su kasance a waje aiki kafin ƙarfe 11 na safe
An ƙiyasta kasafin kuɗin na shekarar 2026 a kan Naira tiriliyan 54.4
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-zai-shiga-shekarar-2026-da-farawa-da-ciwo-bashin-tiriliyan-17/
Hakazalika, Tinubu ya nemi Majalisar ta soke tare da sake tabbatar da kasafin kuɗin 2024 wanda ya kai Naira tiriliyan 43.56.
Manufar wannan mataki ita ce kada a yi aiki da kasafin kuɗi da yawa a lokaci guda, sannan a tabbatar da bin diddigin kashe kuɗi, musamman a ayyuka masu buƙatar kulawar gaggawa da tsaron ƙasa.
Rarraba kasafin kuɗin 2024 ya nuna Naira tiriliyan 1.74 don sauya doka, Naira tiriliyan 8.27 don biyan bashi, Naira tiriliyan 11.27 don kashe kuɗin yau da kullum wanda ba na bashi ba, da kuma Naira tiriliyan 22.28 don ayyukan ci gaba da gudunmawar asusun raya ƙasa.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/sakon-obasanjo-ga-tinubu-abin-kunya-ne-gwamnati-mai-%c6%99arfin-iko-ta-rika-sulhu-da-%c6%b4an-bindiga/
An tsara wannan shiri ne don ƙarfafa tsari wajen kashe kuɗi da tabbatar da cewa kuɗaɗen ana amfani da su kamar yadda Majalisar ta amince.
Masana sun yi gargaɗin cewa tsawaita kasafin kuɗi na iya haifar da ruɗani, maimaitawa, da rashin tsara ayyuka yadda ya kamata, wanda zai iya shafar ci gaban tattalin arziƙi da kuma amincewar masu zuba jari.

