Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu zai bar Abuja a gobe Alhamis 14 ga watan Augusta 2025 domin ziyartar ƙasashen Japan da Brazil, a wani yunkuri na ƙarfafa dangantakar diflomasiyya,da haɓaka tattalin arziƙi, da jawo hankalin masu zuba hannun jari zuwa Najeriya.
A cewar Fadar Shugaban Ƙasa, ziyarar za ta haɗa da manyan taruka da shugabannin ƙasashe, ‘yan kasuwa, da abokan ci gaba a waɗannan ƙasashe biyu.
TST Hausa ta rawaito cewa Shugaban zai Kuma tattauna kan harkokin kasuwanci,da musayar fasaha,da bunƙasa ababen more rayuwa, da haɗin gwiwa a sassa masu muhimmanci kamar makamashi, da noma da ilimi.
Kafin ya isa Japan, Shugaba Tinubu zai tsaya a birnin Dubai, Ƙasar Hadaddiyar Daular Larabawa, domin wata tattaunawa ta musamman da abokan hulɗa na yankin Gulf.
A Japan, ana sa ran Shugaban zai gana da Firaminista Fumio Kishida tare da halartar tarukan kasuwanci da nufin zurfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Japan.
A Brazil kuma, tattaunawar za ta fi karkata ne kan faɗaɗa haɗin gwiwar ƙasashen Kudanci da kuma haɓaka musayar al’adu da tattalin arziƙi.
Wannan ziyara na cikin shirye-shiryen manufofin ketare na Shugaban Ƙasa domin mayar da Najeriya ginshiƙi a harkokin tattalin arziƙin duniya da ƙarfafa abokantaka da ƙasashen da za su tallafa wa manufofin Renewed Hope Agenda na gwamnatinsa.
Zai tafi kasashen wajen ne a daidai lokacin da ake ta rade radin cewa Tinubu bashi da Lafiya,koda yake fadar shugaban kasa ta musanta jita jitar

