Gwamnatin tarayya ta ce Shugaba Tinubu zai kashe naira miliyan dubu 845 da miliyan dari 284 da doriya domin biyan mafi karancin albashin ma’aikata na naira 70,000.
An ware kudaden ne a cikin kasafin kudin shekarar 2025.
Kasafin kudin shekarar ta 2025, wanda shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya gabatar wa majalisar tarayya,yanzu haka yan majalisar sunyi masa Karatu na farko da na biyu , kafin su tafi hutun kirsimati da sabuwar shekara.
Da zarar sun dawo hutu ake sa ran zasu amince da kasafin ,bayan maikatun gwamnatin tarayya da hukumomi sun kare abinda aka ware musu .
A ranar 14 ga watan Janairun shekarar 2025 majalisar ta kasa zata koma aiki.
Kasafin kudin ya tanadi naira biliyan 10 da miliyan dari 955 da doriya domin warware bashin yan kwangilar cikin gida.
Bugu da kari gwamnatin tarayya ta ware naira biliyan 100 domin gudanar da ayyukan ‘Operation zaman Lafiya Dole’ a kokarin samar da zaman lafiya a yankin Arewa maso yamma da Arewa maso gabas.
Shugaban kasa Tinubu a yayinda yake gabatar da kasafin ya tabbatarwa ma’aikatan Najeriya cewa ,zasuci gaba da cin gajiyar romon Demokaradiyya a iya tsawon wa’adin Mulkinsa.
A wata hira da manema labarai, Mataimakin Shugaban majalisar dattawa Sanata Barau Jibiril ya tabbatarwa da yan Najeriya cewa majalisar zata sanya ido dan ganin an aiwatar da kasafin yadda ya kamata.

