Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya yi kira ga shugabannin kasashen yammacin Afirka(ECOWAS )da suyi koyi da siyasar Ghana musamman yadda akayi zaben kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.
Tinubu ya jaddada muhimmancin cigaban dimokuradiyya da hadin kan kasashen Afurika na yamma domin bunkasa yankin.
Shugaba Tinubu, wanda shi ne shugaban hukumar shugabannin kasashe da gwamnatocin kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afurika ta ECOWAS, ya yi wannan jawabi ne a babban taron.kungiyar karo na 66 da aka gudanar a Abuja
A cewar wata sanarwa da mai baiwa Shugaban kasa shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Bayo Onanuga ya fitar, shugaba Tinubu ya yabawa al’ummar Ghana da shugabansu mai barin gado, Nana Akufo-Addo, bisa yadda suka tashi tsaye aka bar jama’a suka zabi wanda suke so da kuma yadda Demokaradiyya tayi aikinta
Shugaba Tinubu ya kuma yabawa shugaba Akufo-Addo mai barin gado bisa jagorancinsa na kwarai da kuma jajircewarsa ga kungiyar ECOWAS a tsawon wa’adinsa na shekaru biyu da ya rike Kungiyar yana mai bayyana shi a matsayin babban mai kishin Afurika.
Shugaba Tinubu ya kuma taya gwamnati da al’ummar kasar Senegal murnar nasarar zaben ‘yan majalisar dokoki da suma sukayi a kasar.
Ya yabawa Ministar harkokin wajen Ghana, Shirley Ayokor Botchwey, kan yadda ta jagoranci kwamitin ministocin ECOWAS na kawo sauyi.
A wa’adinsa na biyu a matsayin Shugaban ECOWAS, Shugaba Tinubu ya bayyana nasarorin da aka samu a wa’adinsa na farko, da suka hada da ci gaban yankin, da bunkasar tattalin arziki, da magance rikice-rikice, da yaki da ta’addanci.

