Shugaban kasa Bola Ahamad Tinubu yayi watsi da bukatar kashe naira biliyan 942 da hukumar kidaya ta kasa ta gabatar domin gudanar da kidayar gidaje da yawan jama’a ta kasa.
Wata majiya da ta nemi a boye sunanta ta tabbatar dacewa , Shugaban kasa Tinubu ya nemi lalle da hukumar kidayan ta Najeriya ta koma ta rage yawan kuɗin da take bukatar kashewa.
Haka kuma bayan ganawar da akayi tsakanin shugaban hukumar kidayan ta Najeriya Alhaji Nasir Kwarra, Tinubu ya yi alkawarin kafa wani kwamitin da zai daidaita kuɗaden da aka gabatar masa domin yin aikin kidayar jama’ar.
Mataimaki na musamman ga shugaban kasa kan harkokin yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, a wata sanarwa da ya fitar mai taken, ‘Najeriya ta matsa kusa da sabuwar kidayar jama’a, yace shugaba Tinubu ya kafa kwamiti,’ da zai bashi shawara kan yadda za’ayi aikin.
TST Hausa ta rawaito cewa yau kimanin shekaru 19 kenan ba’a sakeyin kidayar jama’a a Najeriya ba ,kuma abisa dokar kasa a shekarar 2016 zamanin mulkin Muhammadu Buhari ya kamata ace anyi kidayar.
Koda yake a shekarar 2023 ma an shirya gudanar da kidayar,saidai a wancan lokacin ma an dage ,Inda tsohon shugaban kasa Buhari yace wanda zai gajeshi shine zai shirya kidayar.
A yanzu haka Tinubu yace ana gab da kammala shirye shiryen gudanar da aikin kidayar,kuma yayi alkawarin amfani da matasa masu yiwa kasa hidima na NYSC wajen gudanar da aikin.

