Shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu ya nada Vice Admiral Ibokette Ibas mai ritaya,a matsayin gwamnan Jihar Rivers na rikon kwarya na tsohon watanni 6.
Idan za’a iya tunawa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya dakatar da gwamnan jihar da mataimakiyarsa da yan majalisar dokokin jihar bayan sanya dokar ta-ɓaci a jihar Rivers bayan rikita-rikitar siyasa da jihar ta daɗe tana fama da shi.
Shugaban ya ayyana hakan ne a jawabin da ya gabatar a kan matsalar siyasar da ke addabar jihar ta Rivers.
Gwamnan jihar Siminalayi Fubara da majalisar dokokin jihar sun kasa samun fahimtar juna a tsawon lokaci.
Bayan nazari kan halin da ake ciki a jihar Rivers, ya zama wajibi na sashi na 305 na ayyana dokar ta-ɓaci daga yau 18 ga watan Maris, 2025
An dakatar da gwamnan Siminalayi Fubara da mataimakiyarsa na tsawon wata shida.
Tinubu yace yayi iyakar bakin kokarinsa kan yadda za a magance matsalar to amma duka bangarorin sun yi watsi da yunkurin nasa
Haka nan shugaban ƙasa ya bayyana cewa wasu mutane daga ɓangarori daban-daban su ma sun yi nasu kokarin amma babu mafita.
A yanzu ta tabbata babu wata sahihiyar gwamnati a jihar Rivers.

