Close Menu
  • Shafin Farko
  • Labarai
  • Ketare
  • Siyasa
  • Noma da Kiwo
  • Yanayi
  • Tsaro
  • Karin Wasu
    • Kasuwanci
    • Ilimi
    • Nishadi
    • Muhalli
    • Lafiya
    • Ra’ayi
    • Wasanni
Facebook X (Twitter) Instagram WhatsApp Telegram
TST HAUSATST HAUSA
  • Shafin Farko
  • Labarai

    HUDUBA: Alfahari da Aikin Alheri Babban Kuskure Ne — Dr. Aliyu Yunus

    June 5, 2026

    NAHCON na duba yiyuwar fara da Dawo da Alhazan Kano da suka yi Korafin Guzurinsu ya Kare kuma suka kosa da Zaman Makka

    June 4, 2026

    NOA Ta Karrama CPS na Gwamnan Kano a Matsayin “Dan Najeriya na Mako” Kan Mayar da Riyal 6,000 da Aka Yi Masa Kuskuren Biya A Makka

    June 4, 2026

    Saudiyya Na Fitar da Lita Miliyan 1.6 na Ruwan Zamzam a Kullum Domin Hidimtawa Mahajjata a Hajjin 2026

    June 3, 2026

    Saudiyya Ta Fara Rabon Alƙur’ani Mai Tsarki Miliyan 1.9 Ga Alhazan Da Suka Kammala Aikin Hajjin Bana

    June 2, 2026
  • Ketare

    Yau Ake Toshe Shafukan Sada Zumunta na Yara yan Kasa da Shekara 16 a Australia

    December 4, 2025

    Rikicin Gaza:Sarkin Saudiyya ya amincewa Falasdinawa 1000 su shiga kasar su sauke farali kyauta

    May 19, 2025

    Duk wanda ya yarda zai bar Amurika ya koma kasarsa zamu bashi kyautar Dala 1000 – Inji Trump

    May 6, 2025

    Ba a ga jinjirin watan Shawwal a Saudiyya ba

    March 29, 2025

    An ga watan Sallah karama a Saudiyya

    March 29, 2025
  • Siyasa

    Na Rungumi Kaddara kan Rasa Takarar Kujerar Majalisar Tarayya a Gezawa da Gabasawa – Hon. Dan Malam

    May 8, 2026

    Kofa Har Yanzu a Buɗe Take ga Kwankwaso Ya Koma PRP, Tunda Akwai Shakkun Samun Mafita a NDC – In Ji Ali Rabiu Ali

    May 4, 2026

    Kwankwaso bai kammala Takaba a ADC ba ya koma NDC – In Ji Kwamared Waiya

    May 3, 2026

    Kwankwaso Ya Shiga Tattaunawa da NDC da PRP Kan Sabuwar Makomarsa a Siyasa

    May 3, 2026

    Ni rigimammen ɗan siyasa ne, masu neman amfani da matsalar tsaro su kayar da ni a 2027 ba za su yi nasara ba – Tinubu

    April 29, 2026
  • Noma da Kiwo

    Za’a samu ƙarancin shinkafar Basmati da Indiya ke nomawa a bana

    September 4, 2025

    Tsadar rayuwa: Komai matsayin mutum a Najeriya ya koma gona,saboda abinda na hango -Inji wani Lauya

    December 15, 2024
  • Yanayi
  • Tsaro

    Yan Bindiga Sunyi garkuwa da ’yan uwan Mataimakin Gwamnan Sokoto

    May 1, 2026

    An Kama Budurwa da Kunkuru 30 a Filin Jirgin Sama Ta Na Ƙoƙarin Shiga Jirgi da Su

    April 30, 2026

    A Wasan Hausa na koyi yadda ake sace Mutane – In ji Matashin da DSS suka kama a Kano

    February 13, 2026

    Duk wanda ya Kashe Wani a nemi shawarar Malamai a aika shi Lahira Kawai – Sheikh Daurawa

    January 18, 2026

    An sako Yan Mauludi 28 da aka sace tun 2025 a Filato

    January 10, 2026
  • Karin Wasu
    1. Kasuwanci
    2. Ilimi
    3. Nishadi
    4. Muhalli
    5. Lafiya
    6. Ra’ayi
    7. Wasanni
    8. View All

    Yan Najeriya basa shayin kashe Kudi, sunyi amfani da Fetur na Naira Tiriliyan 1.58 a Bikin Kirsimeti -In Ji Gwamnatin Tinubu

    January 22, 2026

    Dangote ne ya rage farashin fetur da kaso 5.6%, shi ya sa farashi ya sauka ba saboda janye harajin 15% ba.

    November 19, 2025

    Dangote ya buɗe sabon kamfanin siminti mai darajar CEFA biliyan 100 a Côte d’Ivoire

    October 13, 2025

    Dangote ya ƙaddamar da gina kamfanin takin zamani na dala biliyan 2.5 a Habasha

    October 4, 2025

    Ɗan Najeriya daga Kano ya shiga cikin manyan masana yanayi na duniya ,zai halarci taro a Caribbean

    April 28, 2026

    Har Yanzu Akwai Dama Ta Neman Daren Lailatul Qadr — Limamin Harami A Makkah Ya Ja Hankalin Musulmi A Juma’ar Karshe Ta Ramadan

    March 13, 2026

    Ayyukan Cigaban Ilimi a Kano Sun Wuce Zato, Gwamna Yusuf Ya Sauya Alkibla – Kwamared Waiya

    February 25, 2026

    Marubuciyar Najeriya, Dr Asma’u Isah Maibasira, Ta Kaddamar da Littafin Jagoranci a Birtaniya

    February 7, 2026

    An Amince da Fara Shirya Fim ɗin Maitatsine – Darakta

    January 9, 2026

    Karamin Yaron da Kakarsa Ta yi Sanadiyar Daukakarsa a Duniya ya Cika Shekara 12

    December 14, 2025

    MUTU KA RABA — HISBA ta ce aure tsakanin Mai Wushirya da ‘Yar Guda ba ta dauke shi da wasa ba

    October 21, 2025

    Majalisar Yara: Gwamna Yusuf ya baiwa yara aron zaman majalisar zartaswarsa a Kano dan girmama Ilimi

    January 13, 2025

    Majalisar dokokin Kano ta amince da dokar cin tarar kuɗi ga duk wanda ya sake tofar da yawu ko majina akan hanya

    February 3, 2025

    Sauyin Yanayi: Gwamnatin Kano ta dauki sabbin matakan kare Muhalli

    January 31, 2025

    Daga yanzu an daina barin tilin shara akan titunan birnin Kano – Gwamnatin Kano

    January 13, 2025

    Da ’Yan Najeriya Sun San Haɗarin Abincin da Ake Shanyawa a Gefen Hanya, Ko Kyauta Aka Ba Su Ba Za Su Ci Ba — Masana

    January 30, 2026

    WHO Ta Yi Kira Da A Kara Haraji Kan Barasa Da Abubuwan Sha Masu Dauke Da Sikari

    January 14, 2026

    Tinubu Naira 10,400 kacal ya warewa kowane ɗan Najeriya a fannin lafiyarsa cikin kasafin kuɗin 2026 – NMA

    December 29, 2025

    Gwamna Yusuf ya amince da Kashe kuɗi naira miliyan 164 domin sake gyara Asibitin Asiya Bayero

    November 2, 2025

    Ya kamata Hisba da Malamai a Kano su bayyana matsayinsu kan yadda yan siyasa ke jifan juna da kalmar LUWADI – Anas Hassan

    February 24, 2025

    Labarin dan Jaridar da ya kafa tarihi a duniyar yada labarai a kafar sadarwa ta zamani

    February 3, 2025

    Burinmu a yanzu shine Barau FC ta samu gurbin shiga gasar zakarun Nahiyar Africa – DSP Barau

    February 25, 2025

    An karrama jagoran kwallon kafa na Barau Jibiril Academy da lambar gwarzon shekara a bangaren Shugabanci

    December 21, 2024

    HUDUBA: Alfahari da Aikin Alheri Babban Kuskure Ne — Dr. Aliyu Yunus

    June 5, 2026

    NAHCON na duba yiyuwar fara da Dawo da Alhazan Kano da suka yi Korafin Guzurinsu ya Kare kuma suka kosa da Zaman Makka

    June 4, 2026

    NOA Ta Karrama CPS na Gwamnan Kano a Matsayin “Dan Najeriya na Mako” Kan Mayar da Riyal 6,000 da Aka Yi Masa Kuskuren Biya A Makka

    June 4, 2026

    Saudiyya Na Fitar da Lita Miliyan 1.6 na Ruwan Zamzam a Kullum Domin Hidimtawa Mahajjata a Hajjin 2026

    June 3, 2026
TST HAUSATST HAUSA
Home » Tinubu ya jinginar da Najeriya,dole a biya naira dubu 250 maifi karancin albashi,zamu fita zanga zanga 1 ga watan Augusta 2025 – Yan kishin ƙasa
Labarai

Tinubu ya jinginar da Najeriya,dole a biya naira dubu 250 maifi karancin albashi,zamu fita zanga zanga 1 ga watan Augusta 2025 – Yan kishin ƙasa

By tstJuly 23, 20253 Mins Read
Facebook Twitter WhatsApp
IMG 20250723 WA0014

Kungiyar yan kishin Najeriya,wato Nigeria patriotic front movement (NPFM) sun sake shirya zanga zangar lumana a sassan Najeriya daga ranar 1 ga watan Augusta na shekarar 2025.

A wani taron manema labarai da Kungiyar ta yan kishin Najeriya karkashin jagorancin shugabanta Kwamared Abdulmajid Yakubu Daudu ta shirya a birnin Kano ta bayyyana wasu daga cikin dalilan sake komawa zanga zangar makamanciyar wacce suka shirya a ranar 1 ga watan Augusta na shekarar 2024.

Kwamared Abdulmajid yace zasu koma Zanga zangar ne domin tunawa da wadanda suka mutu ko suka bace a zanga-zangar da ta gudana a shekarar da ta gabata, da kuma sake jaddada bukatar kawo karshen mulkin rashin adalci da kuma tsadar rayuwa da ke gallaza wa ‘yan Najeriya.

Kungiyar yan kishin Najeriya sun ce a yayin zanga zangar zasu sake gabatar da Muhimman Abubuwan ga Shugaban kasa da suka hada :

1. Adalci ga waɗanda suka mutu ko suka bace a 2024

Kungiyar ta bukaci gwamnati ta yarda cewa ta kashe fararen hula da ba su da laifi, ta nemi gafara, sannan ta biya diyyar dangi da iyalan da abin ya shafa.

2. Gyara fannin tsaro:

Fiye da mutane 2,124 aka sace daga Janairu zuwa Yuli 2024, inda aka biya fiye da naira miliyan 389 a kudin fansa.

Jihohin da suka fi fuskantar matsalar sace mutane sun hada da Zamfara (667), Kaduna (454), da Neja (253).

Mutane 10,217 sun mutu cikin shekaru biyu na mulkin Shugaba Tinubu, a cewar Amnesty International.

‘Yan sanda da sojoji ba sa samun kayan aiki da albashi mai kyau duk da hadarin da ke tattare da aikinsu.

3. Saukin rayuwa da rage farashin kayayyaki.

Farashin abinci da mai sun yi tashin gwauron zabo, yayin da albashi da kudin shiga na mutane ya tsaya cik.

4. Kawowa da gaggawa ga cin hanci da rashawa.

Ana yi wa wasu rufa-rufa yayinda ake tursasawa wadanda ba sa goyon bayan gwamnati.

Kungiyar na bukatar a rage yawan kudaden da gwamnati ke kashewa wajen biyan ‘yan siyasa.

5. Mayar da manyan kamfanonin gwamnati na zamani:

A dawo da NNPC, lantarki, da kamfanin sadarwa na NITEL hannun gwamnati don samar da ci gaban masana’antu da kare kasa.

6. Albashi mafi karanci na gaskiya:

A kai albashin mafi kankanta zuwa ₦250,000 a kowane wata.

A biya duka hakkokin yan fansho da kudin ritaya.

7. Dakatar da kwace gonakin talakawa:

Kungiyar ta zargi manyan masu rike da madafun iko da kwace filaye da gonaki, musamman a Arewacin Najeriya, lamarin da ke kara rikicin tsaro.

8. Ilmi na kowa da kowa:

A tabbatar da cewa kowa zai iya samun ilimi ba tare da biyan bashin karatu ba. A mayar da bashin karatu zuwa tallafi.

9. Dakatar da sabbin bashin kasashen waje

NPFM ta nuna damuwa da yadda bashin Najeriya ya haura dala biliyan 46 a 2025, duk da cewa an share duka bashin a zamanin Obasanjo.

Kungiyar ta zargi Shugaba Tinubu da kinkin kin sauraren koke-koken jama’a tun bayan zanga-zangar da aka yi a bara, inda ya zargi matasa da tada zaune tsaye maimakon daukar matakan rage tsadar rayuwa.

Ta kuma bayyana cewa jam’iyyar APC ta mamaye sauran jam’iyyun adawa, kuma hakan yana yi wa tsarin dimokuradiyya zagon kasa. Ta bayyana gwamnati a matsayin “Mai nuna karfi da iko ba tare da bin doka ba.”

Kira ga ‘Yan Najeriya:

NPFM ta jaddada cewa zata ci gaba da gwagwarmaya ta lumana duk da yiwuwar barazana ko farmakin jami’an tsaro.

Kungiyar ta jaddada cewa babu ci gaba da za a samu sai da shugabanni masu kishin kasa.

Share. Facebook Twitter Email Telegram WhatsApp

Related Posts

HUDUBA: Alfahari da Aikin Alheri Babban Kuskure Ne — Dr. Aliyu Yunus

June 5, 2026

NAHCON na duba yiyuwar fara da Dawo da Alhazan Kano da suka yi Korafin Guzurinsu ya Kare kuma suka kosa da Zaman Makka

June 4, 2026

NOA Ta Karrama CPS na Gwamnan Kano a Matsayin “Dan Najeriya na Mako” Kan Mayar da Riyal 6,000 da Aka Yi Masa Kuskuren Biya A Makka

June 4, 2026

Saudiyya Na Fitar da Lita Miliyan 1.6 na Ruwan Zamzam a Kullum Domin Hidimtawa Mahajjata a Hajjin 2026

June 3, 2026
Add A Comment
Leave A Reply Cancel Reply

SABBIN LABARAI

HUDUBA: Alfahari da Aikin Alheri Babban Kuskure Ne — Dr. Aliyu Yunus

June 5, 2026

NAHCON na duba yiyuwar fara da Dawo da Alhazan Kano da suka yi Korafin Guzurinsu ya Kare kuma suka kosa da Zaman Makka

June 4, 2026

NOA Ta Karrama CPS na Gwamnan Kano a Matsayin “Dan Najeriya na Mako” Kan Mayar da Riyal 6,000 da Aka Yi Masa Kuskuren Biya A Makka

June 4, 2026

Saudiyya Na Fitar da Lita Miliyan 1.6 na Ruwan Zamzam a Kullum Domin Hidimtawa Mahajjata a Hajjin 2026

June 3, 2026

Saudiyya Ta Fara Rabon Alƙur’ani Mai Tsarki Miliyan 1.9 Ga Alhazan Da Suka Kammala Aikin Hajjin Bana

June 2, 2026
Advertisement
© 2026 TST HAUSA Developed by ENGRMKS & CO..
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy

Type above and press Enter to search. Press Esc to cancel.