A wata tattaunawa da ya yi da shugaban Faransa Emmanuel Macron a Palais des Élysée Shugaba Bola Tinubu ya jaddada aniyar gwamnatinsa na ba da fifiko ga ilimin yaran Najeriya.
Tinubu ya bayyana wasu tsare-tsare na rage yawan yaran da ba sa zuwa makaranta ta hanyar sabbin manufofinsa na bunkasa ilimi a Najeriya.
Shugaba Tinubu, a cikin wata sanarwa da mai magana da yawunsa Bayo Onanuga, ya fitar, ya bayyana irin kokarin da gwamnati ke yi na samar da tsarin tallafi wanda zai tabbatar da cewa yaran da suka isa makaranta sun koma cikin aji yana mai jaddada rawar da za ta taka da kuma sanin makamar aiki a shirin.
A yayinda ya mayar da jawabi shugaba Macron Faransa ya amince da gagarumin ci gaban da Najeriya ke da shi da kuma muhimmancin saka hannun jari a harkokin ilimi.
Ya kuma magantu a kan abubuwan da ya faru a lokacin horo na watanni shida a ofishin jakadancin Faransa a Najeriya, ciki har da ziyarar jihohin Legas da Kano.

