Shugaban Ƙasa, Bola Ahmad Tinubu, ya mika saƙon ta’aziyya ga ‘yan kasuwa da al’ummar Jihar Kano sakamakon gobarar da ta tashi a Kasuwar Singa a ƙarshen mako.
Gobarar wadda ta fara da yammacin ranar Asabar ta ci gaba da ƙonewa shaguna har zuwa safiyar Lahadi, inda ta lalata sashen kasuwar kayan abinci tare da haddasa asarar dukiya mai yawa.
Shugaban ƙasar ya tuntubi Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, domin samun rahoton halin da ake ciki.
Ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuƙa, musamman ganin cewa wannan na zuwa ne kasa da makonni biyu bayan wata gobara da ta lalata shaguna da dama a kasuwar.
Dangane da haka, Shugaba Tinubu ya bayar da umarnin a gudanar da cikakken bincike domin gano musabbabin gobarar, tare da ɗaukar matakan da za su hana maimaituwar irin wannan lamari da ke jefa ‘yan kasuwa cikin asarar jari da damuwa.
Sanarwar ta fito ne ta hannun Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, a ranar 15 ga Fabrairu, 2026.
Tinubu ya koma nemi da a zurfafa bincike domin gano musabbabin tashin gobarar domin daukar kwararen matakai

