Fadar Shugaban Kasa ta kare Shugaba Bola Ahmad Tinubu kan abin da ya faru da shi a ƙasar Turkiyya na faduwa kasa da ake yadawa a kafafen Sada zumunta na zamani wanda ya janyo ce-ce-ku-ce.
Mai magana da yawun Shugaban Kasa, Bayo Onanuga, ya bayyana hakan a sanarwar da ya fitar.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/tinubu-ya-umarci-a-gaggauta-bincike-da-hukunta-wadanda-suka-kashe-matar-aure-da-yayanta-a-kano/
Ya ce Shugaba Tinubu ya taka wani ƙarfe da ke ƙasa inda yake tafiya ne , lamarin da ya sa ya ɗan rasa daidaiton jikinsa na ɗan lokaci.
Onanuga ya bayyana abin da ya faru a matsayin cewa ba wani babban abun magana ba ne ,yana mai cewa Shugaban bai fadi ƙasa ba, sai dai kawai ya ɗan yi kokarin saka kafarsa ba daidai ba a inda yake tafiya.
KARIN LABARAI:Yan Najeriya basa shayin kashe Kudi, sunyi amfani da Fetur na Naira Tiriliyan 1.58 a Bikin Kirsimeti -In Ji Gwamnatin Tinubu
Onanuga yace Wannan ba wani babban abu ba ne, sai dai ga waɗanda ke son su yi amfani da hakan haifar da rudani ko bata suna.
Fadar Shugaban Kasa ta jaddada cewa Shugaba Tinubu yana cikin koshin lafiya, kuma ya ci gaba da dukkan ayyukan ziyararsa kamar yadda aka tsara, ba tare da wata matsala ba.

