Kungiyar masana aikin Radiyo da Talabijin ta Najeriya SNB reshen Arewa maso yamma na gudanar da taron karawa juna sani na kwanaki biyu ga yan jarida da suka fito daga jihohin Arewa maso yamma.
Taron karawa juna sanin mai taken “kalubalen dake gaban yan Jarida wajen yin bincike da tattara bayanai”sashen koyan aikin jarida na jami’ar Bayaro a Kano shine ya shirya taron da hadin guiwar Kungiyar masana aikin Jarida da Talabijin ta kasa NSB reshen Arewa maso yamma.
Shugaban Kungiyar ta NSB ta Najeriya Farfesa Umaru Fate wanda shine babban bako mai jawabi ,ya fara ne da yiwa mahalarta taron barka da zuwa sannan Kuma yayi fatan yan Jaridar da suka halarci taron zasuyi amfani da abinda suka koya.
Dukannin yan Jaridar da suka halarci taron mambobi ne a kungiyar ta NSB.
A wata sanarwa da Sakataren Kungiyar ta NSB ta Najeriya reshen Kano,Adamu Ibrahim Dabo ya fitar yace a kalla Yan jarida 36 ne zasu amfana da bada horon ,a matsayin kashi na farko.
Taron ya samu halartar manyan baki,ciki harda kwamishinan yada labarai na Kano Kwamared Ibrahim Abdullahi Wayya,da Shugaban Kungiyar na kasa Farfesa Umaru Fate da mataimakin Shugaban Kungiyar ta NSB reshen Arewa maso yamma, Alhaji Ado Sa’idu Warawa da shugabanninta na Jihar Kano da bangaren Shugabancin jami’ar Bayaro da Dr Sule Ya’u da tsohowar Shugabar Kungiyar ma’aikatan yada labarai ta kasa BON kuma tsohowar Shugabar gidan Talabijin na ARTV Hajiya Sa’a Ibrahim da Shugabar gidan Radio da Talabijin na Muhasa Hajiya Aishatu Sule da sauransu.
Taron wanda ke gudana a dakin taro na center for excellent a jami’ar Bayaro,zai kammala ne ranar Talata 28 ga watan Janairun shekarar 2025.

