Shugaban karamar hukumar Gwale Hon Abubakar Muazu Mojo yayi barazanar ajiye aikinsa na shugabancin karamar hukumar muddin ba’a sauya mas a daraktan Mulki na karamar hukumar ba .
Tuni dai Shugaban karamar hukumar ta Gwale Hon Mojo ya bada umarnin a rufe ofishin daraktan Mulki da akafi sani da DPM na karamar hukumar Alhaji Danjuma Zubairu Bebeji.
A Wani sakon murya da Hon Mojo ya akewa da TST Hausa yayi ikirarin cewa idan har Daraktan Mulkin bai bar karamar hukumar ba to shi zai bar masa wajen .
Ya kara dacewa manufofin Daraktan Mulkin sun saba da tsarin kwankwansiyya na yiwa jama’a hidima da taimakonsu .
TST Hausa ta rawaito cewa mutanan biyu sun jima suna takun Saka tun lokacin da Hon Mojon ke Shugaban riko na karamar hukumar Gwale kafin a zabeshi a watan Oktoba .
Daga cikin zarge zargen da Shugaban karamar hukumar Gwale Hon Abubakar Muazu Mojo yake yiwa Alhaji Danjuma Bebeji harda yiwa karamar hukumar zagon kasa da hana tafiyar da aiki yadda ya kamata .
Sauran tuhume tuhume da Hon Mojo ke yiwa Daraktan Mulkin sun hada da sakaci a wajen aikinsa har wasu mahimman takardu suka bata.
Shugaban karamar hukumar Gwalen yace duka shida kansilolinsa da masu bashi shawara zasu sauka ,su barwa Daraktan karamar hukumar muddin ba’a sauya shi ba ,an kawo Wanda zai rika sairaren koken jama’a
Duk kokarin da TST Hausa tayi dan zantawa da Daraktan Mulkin na karamar hukumar yaci tura .

