Farfesa Mahmood Yakubu, Shugaban Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa, INEC, bai mutu ba.
Mista Rotimi Oyekanmi, Babban Sakataren Yada Labarai na Farfesa Yakubu shine ya tabbatar da hakan Inda ya yi Allah-wadai da rahotannin da ake yadawa a kafafen sada zumunta, na rasuwar shugaban zaben a kasar waje
A wata sanarwa da ya fitar a Abuja, Oyekanmi ya ce hukumar ta ja hankalin yan Najeriya kan labarin karya da wani sashe na kafafen sada zumunta ya yada yana ikirarin mutuwar Shugaban hukumar ta INEC.
A cewar sa, labarin ya fara bayyana ne a ranar Litinin 9 ga watan Disamba.
Ya nemi Yan Najeriya suyi watsi da labarin.
Yace maganar gaskiya ma Farfesa Yakubu bai yi tafiya zuwa London ba a cikin shekaru biyu da suka wuce.

