Matashin dan siyasa daga gidan Kwankwasiyya a jihar Kano Hon.Alhaji Rufa’i Nasidi Gambo ya bayyana gamsuwarsa akan sauye sauyen da gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi a kunshin gwamnatinsa.
Ya shaida hakan ne a ganawarsa da manema labarai a birnin Kano.
Yace idan aka duba kwamishinonin da aka sauyawa wuraren aiki , za’a iya cewa a yanzu kwalliya na biyan kuɗin sabulu.
“Idan kuka duba a yanzu kamar wata allura akayiwa kwamishinonin gwamna Yusuf musamman ma’aikatar ilimi an samu sauyi ,sannan haka itama ma’aikatar muhalli da mata da ma’aikatar kula da ayyuka na musamman da ma’aikatar sufuri da ma’aikatar kasuwanci da ta samu Alhaji Shehu Wada Sagagi da sauransu”,Inji Gambo
Ya nemi gwamnan jihar Kano Alhaji Abba Kabir Yusuf ya ci gaba da yin sauye sauyen wuraren aiki a lokaci zuwa lokaci ga kwamishinoninsa domin cigaban jihar Kano.
Da aka tambayeshi kan ko menene dalilin da yasa Alhaji Gambo bai samu mukami a cikin gwamnatin Kano ba?,sai yace bai nema ba kuma baya nema,yana mai cewa yana yin hidima da biyayya a kwankwansiyya sama da shekara 20 ba dan a bashi mukami ba.
Alhaji Rufa’i Nasidi Gambo ya kara dacewa,babu wani bangare a cikin gwamnati da baya bada gudun mowa idan akwai bukatar hakan.
Yace zama a cikin tafiyar Kwankwasiyya kadai ko ba mukami daraja ce.

