Kungiyar yaki da cin hanci da rashawa ta kasa (SERAP) ta yi kira ga shugaban kasar Amurika Donald Trump da ya gano tare da dawo da kudaden almundahana da tsaffin Shugabannin Najeriya da yan siyasa suka sata suka boye a Amurika.
A ranar Litinin din nan 20 ga watan Janairun shekarar 2025 ake rantsar da Donald Trump a matsayin Shugaban Amurika na 47.
Kungiyar ta nemi sabon Shugaban da ya fara takan yan siyasar Najeriya da suka sace arzikin Kasar nan suka boye a Amurika.
SERAP ta kuma bukaci Trump da ya tabbatar da cewa duk wani abin da aka dawo da shi dole ne ya bi ka’idoji masu tsauri na gaskiya da rikon amana, tare da tabbatar da cewa an yi amfani da kudaden ne kawai domin amfanin yan Najeriya.
Kungiyar wacce ta gabatar da wannan bukata a wata wasika mai dauke da sa hannun mataimakin daraktanta na kasa Kolawole Oluwadare, ta shaida cewa ana zargin manyan yan siyasar Najeriya da wawashe kudaden al’umar Kasa tare da boyesu Amurika.
SERAP din ta shaidawa Trump cewa ,ya sa ni Amurika ta zama maboyar kudaden yan siyasa masu cin hanci da rashawa daga Najeriya.
Kungiyar ta ci gaba da cewa, wannan matakin zai cika alkawurran da Amurka ta dauka na taimakawa Najeriya a kokarin kwato kadarorin al’umar kasa da aka boye acan.
Kungiyar ta yi ikirarin cewa hatta kadarorin tsuhuwar ministar man fetur ta Najeriya Diezani Alison-Madueke da aka dawo da su a baya-bayan nan, daga Amurika,sun nuna kadan ne daga cikin sama da dala biliyan 500 da ake zargin ta sace ta boye a Amurikan.
SERAP ta yi nuni da cewa, tana wannan fadi tashin ne domin kare bukatun yan Najeriya da kuma bin ka’idojin Majalisar Dinkin Duniya kan yaki da cin hanci da rashawa, wanda Amurka da Najeriya duka masu kyamar hakan ne.

