An bukaci al’umma su fara sanin kan su kafin su yi kokarin sanin wani abu, a ruyuwar su wanda ta haka ne, za su sami cigaban da ya dace.
Bayanin hakan ya fito ne ta bakin Turakin Kano hakimin Gwale Alhaji Mahmud Ado Bayero a wajan taron GA FILI GA MAI DOKI, wanda sashin Hausa na kwalejin ilmi ta Aminu Kano AKCOE hadin guiwa da jami’ar tarayya ta FUDMA, da kuma kungiyar daliban Hausa karkashin jagorancin kwamared Abubakar Sabo suka yi.
Ya ce idan ta hanyar sanin Kai ne za ka san kana da kima da daraja don haka ya bukaci kowanne bahaushe da ya dinga dabbaka dabi’un sa a duk in da ya sami kan shi, domin nuna cewa ya san kan sa.
Anasa jawabin shugaban makarantar Dakta Ayuba Ahmad Muhammad cewa ya yi, sashin Hausa sun san abun da su ke yi wajan gabatar da ayyukan su don haka za su cigaba da ba su hadin kai da duj wata gudunmawa duk sanda za su gabatar da wani abu, da shafe su.
Anasa bangaren farfesa Sa’idu Muhammad Gusau, bayyana cewa ya ce ana shirya taron ne don a fadi ka’idoji da sharudda da ya kamata a yi waka ta furuci a kuma yi kida a sadar da shi ga al’umma.
Shi kuwa makadin da ya gafarta da kidan shi a wajan Alhaji babangida kakadawa cewa ya yi, dama can yanayin wakokin na sa ne don ilmantarwa da fadakarwa da kuma wa’azantarwa.
Dr Mahe Isah Ahmad shi ne shugaban sashin, na Hausa a makanatar ya ce taron na iya na dalibai ba ne, na duk wani mai kishin Hausa ne, kuma shi ne karo na farko a tarihin kafuwar makarantar.

