Mai alfarma Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji , Sa’ad Abubakar na III, ya sanar da daukacin al’ummar Musulmi a Najeriya cewa za a cika azumin watan Ramadan zuwa kwana talatin, bayan da ba a samu sahihin rahoton ganin jinjirin watan Shawwal ba.
Gidan Radiyon Iconic a Sakoto ya tabbatarwa da TST Hausa hakan ta wayar salula.
Sanarwar ta biyo bayan bayanan da aka tattara daga kwamitocin duban wata a sassa daban-daban na ƙasar nan inda aka tabbatar da cewa babu wanda ya ga jinjirin watan da za a dogara da shi wajen bayyana ƙarshen Ramadan.
KARIN LABARAI:https://tsthausa.com/yanzu-yanzu-baa-ga-watan-shawwal-a-saudiyya-ba-zaa-cika-azumi-30-a-kasar/
Sarkin Musulmin ya buƙaci Musulmi da su ci gaba da azumi a rana ta talatin wato Alhamis 19 ga watan Maris 2026 domin kammala ibadar Ramadan bisa koyarwar addinin Musulunci.
Ya kuma ja hankalin al’umma da su ƙara dagewa da ibada, addu’o’i, da neman gafarar Allah, musamman a wannan rana ta ƙarshe ta watan mai alfarma.
Ana sa ran za a gudanar da Sallar Idi a washegari,wato Juma’a bayan cikar azumin kwanaki talatin, kamar yadda tsarin Musulunci ya tanada.
TST Hausa ta rawaito cewa tunda farko kasar Saudiya ce ta sanar da rashin ganin watan na Sallah karama na bana saboda yadda gajimare ya rufe sararin samaniyar kasar.

