Mai martaba sarkin kano Malam Muhammadu Sunusi na II ya jagoranci raka sabon hakimin Bichi Wamban Kano Alhaji Munnir Sunusi zuwa Ofis.
A wata takarda da mai magana da yawun gwamnan jihar Kano Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa ya sanyawa hannu yace magajin garin Kano Alhaji Nasir Inuwa shine ya wakilci mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sunusi na II wajen raka hakimin Ofis a Bichi.
Ya yabawa al’ummar garin Bichi abisa dafifi da sukayi wajen karbar sabon hakimin nasu.
Da yake jawabi sabon hakimin Bichi Alhaji Munir Sanusi, ya nemi hadin kan al”ummar karamar hukumar domin sauke nauyin da aka dora masa .
TST Hausa ta rawaito cewa raka hakimin nada nasaba da shirye shiryen gudanar da hawan sallah karama a Kano karkashin jagorancin Malam Muhammadu Sunusi na II.

